Gwamna Dauda Ya Karrama Jami'an Rundunar Askarawan Zamfara, Ya Yi Musu Sabon Alkawari

Gwamna Dauda Ya Karrama Jami'an Rundunar Askarawan Zamfara, Ya Yi Musu Sabon Alkawari

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba da ƙwazon da jami'an tsaro na rundunar Askarawan Zamfara suke nunawa a wajen yaƙi da ƴan bindiga
  • Gwamnan ya karrama wasu jami'an rundunar mutum 20 saboda jajircewarsu wajen ganin an kawo ƙarshen ayyukan masu tayar da ƙayar baya
  • Dauda Lawal ya kuma yi alƙawarin kula da dukkanin buƙatun iyalan jami'an rundunar da suka rasa ransu a bakin aiki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya karrama jami’an tsaro 20 na rundunar CPG wacce aka fi sani da Askarawan Zamfara.

Gwamna Dauda ya ba su lambobin yabo ne saboda ƙwazon da suka nuna kuma ya yi alƙawarin tallafawa iyalan waɗanda suka mutu a wajen yaƙi da ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta bayyana matsayarta kan tarar N10 da aka sanya mata kan Aminu Ado

Dauda Lawal ya karrama jami'an tsaro
Gwamna Dauda ya karrama jami'an rundunar Askarawan Zamfara Hoto: @daudalawal
Asali: Twitter

An karrama jami'an Askarawan Zamfara

Gwamnan ya karrama su ne a gidan gwamnati da ke birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Asabar, ta bayyana cewa jami'an tsaron da aka karrama sun taka rawar gani sosai.

Kwamandan rundunar Askarawan Zamfara, Birgediya Janar Lawal Bature Mohammed, shi ne ya jagoranci jami'an tsaron da aka karrama zuwa gidan gwamnati.

Wane alƙawari Gwamna Dauda ya yi?

A yayin jawabinsa wajen karrama jami'an tsaron da aka yi a ranar Alhamis, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada shirin gwamnatinsa na kula da jin daɗin Askarawan.

"Ku ɗauki karramawar da aka yi muku a matsayin hanyar ƙara muku ƙarfin gwiwar ci gaba da wannan muhimmiyar sadaukarwar da kuke yi."
"Ba za mu iya biyan ku ba kan aikin da kuke yiwa jiha da al'umma, abin da kawai za mu iya yi shi ne mu ƙara muku ƙarfin gwiwar ci gaba da nuna ƙwazo."

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi martani yayin da sojoji suka hallaka shugaban 'yan bindiga

"Ina ba ku tabbacin cewa ina da shiri mai kyau a kan iyalan jami'an CPG da suka rasa ransu a bakin aiki. Za mu kula da dukkanin buƙatunsu sannan mu ba su tallafin da ya dace."

- Dauda Lawal

Akwai matsalar rashin tsaro

Legit Hausa ta tuntuɓi wata mazauniyar jihar Zamfara mai suna Zainab Mu'azu wacce ta yaba kan wannan karramawar da gwamnan ya yiwa jami'an tsaron.

Sai dai ta koka da cewa har yanzu matsalar rashin tsaro sai addu'a kawai musamman a inda take zaune watau ƙaramar hukumar Tsafe.

Ta bayyana cewa maƙwabcinsu yanzu haka yana hannun ƴan bindiga kuma an kai kuɗin fansa amma sun ƙi sakinsa, inda suka ƙara buƙatar a ba su babura guda uku.

Gwamna Dauda ya fara biyan sabon albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000 ga ma’aikata a jihar da ke yankin Arewa maso Yamma.

Hakan ya biyo bayan alƙawarin da Gwamna Dauda Lawal ya ɗauka yayin ganawa da shugabannin ƴan kwadago a jihar domin fara biyan sabon alwashin ga ma'aikatan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel