"Kai Waye": Abba Kabir Ya Dauki Zafi Kan Kwamishinan Ƴan Sanda Game da Hana Hawan Sallah

"Kai Waye": Abba Kabir Ya Dauki Zafi Kan Kwamishinan Ƴan Sanda Game da Hana Hawan Sallah

  • Gwamnatin jihar Kano ta magantu kan daukar matakin hana bukukuwan salla da kwamishinan 'yan sanda ya yi a jihar
  • Kwamishinan Shari'a a Kano shi ya kalubalanci kwamishinan ƴan sanda inda ya ke tambayar yaushe ya samu cikakken ikon da zai dauki wannan mataki
  • Wannan na zuwa ne bayan rundunar ƴan sanda a jihar ta haramta gudanar da bukukuwan salla a fadin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta kalubalanci kwamishinan ƴan sanda kan matakin hana bukukuwan sallah a jihar.

Gwamnatin jihar ta ce kwamishinan ba shi da karfin ikon da zai iya hana bukukuwan sallah a fadin jihar baki daya.

Kara karanta wannan

Bayan Dikko Radda ya buɗe kofa, Gwamna a Arewa ya ba ma'aikata N10,000 goron sallah

Abba Kabir ya soki matakin yan sanda na hana hawan sallah a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta kalubalanci kwamishinan ƴan sanda kan hana bukukuwan sallah. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Haruna Kiyawa.
Asali: Facebook

Kano: Abba Kabir ya soki ƴan sanda

Kwamishinan Shari'a a jihar Kano, Haruna Isah Dederi shi ya tabbatar da haka inda hadimin Gwamnan Abba Kabir, Hassan Sani Tukur ya wallafa a shafin X yau Asabar 15 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ya zargi kwamishinan 'yan sanda a jihar da kin bin umarnin gwamnan a matsayinsa na shugaban tsaron jihar.

"Dole na yi wannan tambaya, waye yake neman wuce ikon shugaban tsaron jiha?."
"Saboda wasu sun take umarninsa tare da daukar matakai ba tare da amincewarsa ba ko kwamitin tsaro wurin hana bukukuwan Sallah."
"Ta yaya mutum a cikin hankalinsa zai hana bukukuwan sallah a Kano? Yaushe gwamnan jihar ya bar mukamin shugaban tsaron jiharsa?"
"Ta yaya za a ce Gwamna da kansa sai dai ya ga sanarwar a kafafen sadarwa, waye ya ke tunkuda Kwamishinan wurin wuce gona da iri?."

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: 'Yan sanda sun dauki mataki kan hawan Sallah a Kano

- Haruna Isa Dederi

Gwamnatin Kano ta nemi karin haske

Kwamishinan ya bukaci sanin laifin da ƴan Kano suka yi da ƴan sanda ke neman ruguza ta gaba ɗaya.

Ya ce kwamishinan ƴan sanda a Kano ya dade yana saba umarnin gwamnan a matsayin shugaban tsaron jihar baki daya.

Kano: Ƴan sanda sun hana hawan Salla

A wani labarin, kun ji cewa Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta haramta yin hawa a yayin gudanar da bukukuwan Babbar Sallah mai zuwa a jihar.

Rundunar ta bayyana cewa a yayin bikin babbar Sallah na bana, ba za a yi hawan Sallah ba kamar yadda aka saba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel