Tinubu Ya Bukaci Daraktan Hukuma Dan Arewa da Buhari Ya Nada Ya Yi Murabus
- Shugaba Bola Tinubu ya bukaci Mista Mamman Ahmadu wanda ke jagorancin hukumar BPP ya yi murabus
- Tinubu ya ce hakan na daga cikin himmatuwarsa wurin ingantawa da kuma fadada ayyukan hukumar
- Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci babban daraktan hukumar sa ido a harkokin saye-saye na gwamnati, BPP, Mamman Ahmadu ya yi murabus.
Tinubu ya bukaci hakan ne domin fadada ayyukan hukumar da kuma ingantata da kuma bin diddigi.
Tinubu ya bukaci Ahmadu ya yi murabus
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Asabar 15 ga watan Yuni a shafinsa na Facebook.
Ngelale ya ce Tinubu ya umarci Mamman da ya mika dukkan kayayyakin da ke ofishinsa ga mafi girman matsayi a hukumar.
"Shugaba Tinubu ya mika godiya kan irin gudunmawa da Mista Ahmadu ya bayar inda ya ke masa fatan alheri a rayuwa."
- Ajuri Ngelale
Jim kadan bayan fitar da wannan sanarwa, Bola Tinubu ya maye gurbin Ahmadu da tsohon kwamishina a jihar Lagos, Ayodeji Ariyo Gbeleyi.
Buhari ya nada Ahmadu daraktan BPP
A watan Satumbar shekarar 2016, shugaban kasa na wancan lokaci, Muhammadu Buhari ya nada Mamman Ahmadu a matsayin babban daraktan hukumar BPP.
Buhari ya amince da nadin Ahmadu a hukumar duba da kwarewar da yake da shi na tsawon shekaru.
Sauran wadanda aka naɗa mukaman akwai Dakta Isa Ali Pantami a matsayin babban daraktan hukumar NITDA.
Tinubu ya naɗa Nasiru Gawuna mukami
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada Nasiru Yusuf Gawuna babban mukami a Jami'ar Bayero da ke jihar Kano.
Tinubu ya nada Gawuna muƙamin shugaban kwamitin gudanarwar na Jami'ar bayan sake yin garambawul a mukaman.
Sauran ƴan kwamitim da ke karkashin Gawuna sun hada da Abubakar Dauda da Nora Alo da Ibrahim Obanikoro da kuma Musa Abbas.
Asali: Legit.ng