Hajji 2024: Manyan Abubuwan da Huɗubar Arafa Ta Mayar da Hankali a Kai

Hajji 2024: Manyan Abubuwan da Huɗubar Arafa Ta Mayar da Hankali a Kai

  • A yau Asabar, 15 ga watan Yuni miliyoyin mahajjata daga ƙasashen daban-daban suka gabatar da hawan Arafa a kasa mai tsarki
  • Hawan Arafa yana daya daga cikin manyan ayyukan Hajji da ake bukatar mahajjata maza da mata sa gudanar yayin aikin Hajji
  • Sheikh Mahir Al Muaiqly ne ga gabatar da huɗubar Arafa kuma ya ja hankalin al'ummar Musulmi kan abubuwa da dama

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Miliyoyin mahajjata daga sassan duniya daban-daban sun gabatar da hawan Arafa a yau Asabar.

Sheikh Mahir Al Muaiqly ne ya jagoranci huɗubar Arafa inda ya yi jawabai kan abubuwa masu muhimmanci da suka shafi Musulman duniya.

Kara karanta wannan

Ana gobe sallah, Bola Tinubu ya tura sako na musamman ga 'yan Najeriya

Arafa 2024
Sheikh Mahir Al Muaiqly ya ja hankulan Musulmi yayin hudubar Arafa. Hoto: Inside the Haramain
Asali: Facebook

Legit ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da malamin ya tattauna cikin wani sako da shafin Inside the Haramain ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufar kafa shari'ar Musulunci

A yayin huɗubar Sheikh Mahir ya ce addinin Musulunci ya zo ne domin kawo maslaha da samar da sauki ga al'ummar duniya baki daya.

Ya tabbatar da cewa saboda haka ne shari'a ta ke zaben dukkan abin da zai zama mafi kyau ga rayuwar al'umma da kuma kawar da dukkan abin da zai cutar.

Laduban da ake so daga Musulmi

Malamin ya tunatar da al'ummar Musulmi kan kyawawan dabi'u kamar biyayya ga iyaye da sada zumunta.

Ya kara da cewa ana so Musulmi ya siffanta da dabi'un kiyaye hakkokin mutane, mayar da amana, cika alkawari da biyayya ga shugabanni.

Halin da Falasdinawa ke ciki

Sheikh Mahir ya yi kira kan yan uwa Musulmi su yi addu'a ta musamman ga Falasɗinawa saboda halin da suke ciki.

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya sun kwamushe mutum 18 bisa karya dokar aikin Hajji

Malamin ya ce Falasɗinawa na bukatar taimakon al'ummar Musulmi lura da yadda ake zubar da jininsu kuma aka hanasu bukatun rayuwa na yau da kullum.

Abubuwa 5 da ake so a kiyaye

Malamin ya bayyana cewa Allah ya yi umurni da kiyaye abubuwa guda biyar wanda suka haɗa da kiyaye addini, rai, hankali, dukiya da mutunci.

Ya tabbatar da cewa shari'a ta ba abubuwan muhimmanci ta inda za a iya yin uƙuba da dukkan wanda ya keta su a duniya da lahira.

Kiyaye abubuwan kuma suna sanya mutum ya samu yardar Allah da kuma shiga aljanna a gobe lahira.

Ba siyasa a aikin Hajji

Sheikh Mahir ya ja hankalin mahajjata cewa ana bukatar tsarkake niyya lokacin da ake cikin aikin Hajji.

Saboda haka ya yi kira ga mahajjata kan su sani cewa Harami ba waje ne na tallata yan siyasa ko jam'iyyar siyasa ba.

Kara karanta wannan

Innalillahi, Allah ya yiwa wata hajiya daga jihar Kaduna rasuwa a ƙasa mai tsarki

An bayyana adadin mahajjatan bana

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta ambaci adadin mahajjatan da suke gabatar da aikin Hajjin shekarar 2024 yayin da aka fara gudanar da ibadar..

Rahotanni sun nuna cewa jami'in yada labaran ma'aikatar lafiya ta kasar ya ambaci babbar matsalar da mahajjata za su iya fuskanta yayin Hajjin bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel