Gwamna Ya Yi Martani Yayin da Sojoji Suka Hallaka Gawurtaccen Shugaban 'Yan Bindiga

Gwamna Ya Yi Martani Yayin da Sojoji Suka Hallaka Gawurtaccen Shugaban 'Yan Bindiga

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yabawa rundunar sojojin Najeriya kan gagarumar nasarar da dakarunta suka samu
  • Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka wani gawurtaccen shugaban ƴan bindiga, Buharin Yadi tare da mayaƙansa
  • Gwamnan ya nuna farin cikinsa kan hakan inda ya yi alƙawarin ci gaba da bayr sa goyon baya domin ganin an kawo ƙarshen ƴan bindiga a yankin Arewa maso Gabas

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya yabawa rundunar sojojin Najeriya bisa kashe riƙaƙƙen shugaban ƴan bindiga Buhari Halidu.

Buhari Halidu wanda aka fi sani da Buharin Yadi ya gamu da ajalinsa ne a hannun sojoji tare da wasu ƴan ta’addan da suka kai sama da 30.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta bayyana matsayarta kan tarar N10 da aka sanya mata kan Aminu Ado

Gwamna Radda ya yabawa sojoji
Gwamna Dikko Radda ya yabawa sojoji kan kisan Buharin Yadi Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Sojoji sun hallaka Buharin Yadi

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Nasir Mu’azu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar wacce sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Ibrahim Kaula, ya fitar ta ce an hallaka Buharin Yadi ne a wani samame da sojoji suka kai a yankunan jihohin Katsina da Kaduna.

"Samamen wanda aka kai bayan samun bayanan sirri ya shafi wurare masu muhimmanci a jihohin da suka haɗa da Dorawar Yan Kaji, Ginanna a Katsina, da Samunaka, Sirdi da Kan Dawa a Kaduna."
"Hakan ya ba dakarun sojojin damar bin sawu tare da hallaka shugaban ƴan ta'addan da mayaƙansa."

- Ibrahim Kaula

Gwamna Radda ya yabawa sojoji

Gwamnan ya yaba da jarumtar da sojojin da suka yi aikin suka nuna inda ya nuna muhimmancin rawar da suke takawa wajen dawo da zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya karrama jami'an rundunar Askarawan Zamfara, ya yi musu sabon alkawari

Ya kuma nuna godiyarsa a madadin al'ummar yankin kan ƙoƙarin da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane daga ƴan ta'adda.

Gwamna Dikko Radda ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba su goyon baya a ƙoƙarin da ake yi na kawo ƙarshen ƴan ta'adda a yankin Arewa maso Gabas.

Sojoji na ƙokari sosai

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin jihar Katsina mai suna Muhammad Auwal, wanda ya yaba da namijin ƙoƙarin da sojojin suka yi.

Ya bayyana cewa sojojin na taka muhimmiyar rawa wajen kawo ƙarshen ƴan bindigan da suka addabi mutane.

A kalamansa:

"Eh tabbas sojoji na yin namijin ƙoƙari a yaƙin da yake yi da matsalar rashin tsaro. Muna yi musu fatan nasara a wannan aikin da suke yi na sadaukar da rayukansu.

Ƴan bindiga sun sace ƴan ƙasar waje

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da manajan darakta na kamfanin Fouani mai wakiltar LG da Hisense a Legas.

Ƴan bindigan sun sace manajan ne tare da wasu ƴan kasar Lebanon guda uku a yayin da suke tafiya cikin kwale-kwale a Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel