A Karon Farko a Mulki, Sanusi II Yayi Maganar Rikicin Sarautar Kano da Aminu Ado Bayero

A Karon Farko a Mulki, Sanusi II Yayi Maganar Rikicin Sarautar Kano da Aminu Ado Bayero

  • Muhammadu Sanusi II ya yi magana da manema labarai a wata hira, ya tabo zancen sabanin da aka samu a masarauta
  • Basaraken ya zargi gwamnatin Kano da raba kan gidan dabo, inda aka nada Aminu Ado Bayero bayan an cire masa rawani
  • Sanusi II ya ce dawo da shi kan karaga da rusa kirkirarrun masarautu ya maido da kima da martabar Sarkin Kano mai tarihi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan rigimar da ta shigo masarautar Kano bayan an sauke sarakunan da aka kirkiro a 2019.

A watan da ya gabata gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sa hannu a sabuwar dokar da ta tsige Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano Sanusi II ya yi yayin da aka yanke hukunci a shari'ar Aminu Ado

Sanusi II da Aminu Bayero
Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero na ikirarin sarautar Kano Hoto: @SanusiSnippets, #HRHBayero
Asali: Twitter

Sarki Muhammadu Sanusi II ya bude baki

Muhammadu Sanusi II ya yi hira da jaridar Sun, inda ya bayyana cewa wadanda aka nada bayan sauke shi a 2020 suna jin haushin tsige su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai martaba bai ambaci Sarki Aminu Ado Bayero ba, amma kalamansa suna nuni gare shi ne domin shi aka tsige domin maida shi.

Sanusi II ya ce an raba gidan dabo

"Mu na cikin wani yanayi da wani ya raba mu. Kuma idan aka kawo irin wadannan abubuwa, wasu za su samu wasu damammaki."
"Ba su nema ba, amma sun ci moriyarsa na shekaru hudu."
"Yanzu kuma da suka rasa, ya zama matsala. Amma ba yau aka samu matsalar ba. Tun shekaru hudu da suka wuce, aka haifar da ita."
"Da tun farko ba ayi wannan ba, da ba a kai ga haka a yau ba. Dangi daya ne, mutane guda. Wani ya zo ya rabu."

Kara karanta wannan

Kotu ta daure matashin da ya sace dabbobi, ya kalmashe kudin mutane a aljihu

- Muhammadu Sanusi II

"An dawo da darajar sarautar Kano" - Sanusi II

Daily Trust ta rahoto Sanusi II yana kuka kan yadda aka kacalcala masarautar Kano, aka kirkiro wasu, abin da ba ayi a shekaru 1000 ba.

"Ko a cikin gidan, ya dauki masarauta guda ya ba wani gida. Yanzu da aka karbe daga hannunsu bayan shekaru hudu, ya zama matsala."

- Muhammadu Sanusi II

Sarkin ya ce ba kowa ake hari ba, gwamna ya ga bukatar dawo da kimar masarautar ne, sai dai hakan zai yi wadanda aka sauke ciwo.

Jawabin Sanusi II daf da komawa sarauta

Rahoto ya zo cewa a jihar Ribas ne kalaman karshe da Muhammadu Sanusi II ya yi kafin komawa gidan dabo suka fito a watan jiya.

Sanusi II ya tabo gwamnatin Bola Tinubu, inda ya soki yawan haraji da ake kakabawa, sai aka ji an rusa dokar masarautu a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel