Bola Tinubu Ya Tura Tallafi Ga Gwamna Abba Yayin da Ake Fama da Rikicin Sarautar Kano

Bola Tinubu Ya Tura Tallafi Ga Gwamna Abba Yayin da Ake Fama da Rikicin Sarautar Kano

  • Bola Ahmed Tinubu ya tura kayan masarufi da suka kai tan 2,706 ga gwamnatin jihar Kano domin a rabawa talakawa
  • Hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) ta miƙa tallafin wanda ya ƙunshi masara, dawa da gero ga Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Gwamna Abba ya godewa shugaban ƙasa bisa wannan karamci kana ya buƙaci ya ci gaba da tallafawa al'ummar jihar Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da gudunmawar kayan masarufi da yawansu ya kai tan 2,706 ga gwamnatin jihar Kano

Shugaban ya bada waɗannan tulin kayan abinci ne domin rabawa mutane masu ƙaramin ƙarfi a faɗin kananan hukumomi 44 na jihar.

Kara karanta wannan

Tinubu na yin katsalandan kan ayyukan hukumar EFCC? Gaskiya ta bayyana

Tinubu da Abba Kabir Yusuf.
Shugaba Tinubu ya baiwa Kano gudummuwar kayayyakin abinci Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Daily Trust ta ce Tinubu ya miƙa tallafin da suka hada da masara, gero, dawa da garri ga gwamnatin Kano ta hannun hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu na kokarin rage raɗaɗi

Da take miƙa kayayyakin a madadin Tinubu, Darakta-Janar ta hukumar NEMA, Zubaida Umar, ta jaddada kudirin shugaban kasa na rage raɗaɗin tsadar rayuwa.

A wannan kason, jihar Kano ta samu tan 969 na masara, tan 1,320 na dawa da tan 417 na gero, wanda ake sa ran za a rabawa maɓukata a faɗin jihar.

Daga ciki an ware kashi 20% ga ƙungiyoyin addinai yayin da kaso 3% za a rabawa makarantun kwana.

Zubaida Umar ta yi gargadi game da ambaliyar da aka yi hasashen zata iya faruwa a 2024 duba da hasashen yanayin da aka fitar na shekara-shekara.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: Ana shirin babbar Sallah wasu mutum 19 sun mutu lokaci guda a Arewa

Gwamna Abba ya sha alwashin raba kayan

Bayan karbar kayan, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin bin umarnin gwamnatin tarayya wajen raba kayayyakin.

Gwamna Abba ya yi kakkausar gargadi ga duk wani mai niyyar karkatarwa ko aikata munanan ayyuka a lokacin rabon kayayyakin.

Yayin da ya ke nuna jin dadinsa da karamcin shugaban ƙasar, gwamna ya bukaci ya ci gaba da tallafa wa al’ummar jihar Kano, rahoton Vanguard.

Wanene sahihin Sarkin Kano?

A wani rahoton kun ji cewa yayin da ake ci gaba da rigimar sarauta, kotu ta shirya yanke hukunci kan sabuwar dokar masarautar Kano.

Mai Shari'a Liman na babbar kotun tarayya ya sa ranar 20 ga watan Yuni domin yanke hukunci kan halascin mayar da Sarki Sanusi II.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel