Ana Tsaka da Rigimar Sauratar Kano, Fitaccen Basarake Ya Mutu a Arewa

Ana Tsaka da Rigimar Sauratar Kano, Fitaccen Basarake Ya Mutu a Arewa

  • An shiga jimami bayan rasuwar fitaccen Basarake da ke mulkin Moro’a Asholyio da ke Manchok a jihar Kaduna
  • Marigayi Agwam Tagwai Sambo ya rasu ne yana da shekaru 87 a duniya bayan fama da jinya a jihar
  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin inda ya yi masa addu'ar samun rahama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya tura sakon ta'aziyya bayan rasuwar fitaccen basarake a Kudancin jihar.

Gwamnan ya jajantawa Agwam Tagwai Sambo da ke sarautar Moro’a Asholyio da ke Manchok a karamar hukumar Kaura.

Basarake ya kwanta dama a jihar Kaduna
Fitaccen basarake a jihar Kaduna, Agwam Tagwai Sambo ya kwanta dama. Hoto: @ubasanius.
Asali: Twitter

Kaduna: Uba Sani ya jajanta mutuwar basarake

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Uba Sani ya bayyana haka ne a daren jiya Juma'a 14 ga watan Yuni a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Cikin alhini da mika lamura ga ubangji, mun samu labarin rasuwar basarakenmu mai daraja wanda ya ke son zaman lafiya, Cif Agwam Tagwai Sambo da ke Moro’a Asholyio a Manchok."
"Ya jagoranci mutanensa cikin hikima da jarumta da kuma tausayi, ya tsaya tsayin daka wurin tabbatar da adalci tare da inganta al'ummarsa."
"A madadina da iyalaina da kuma al'ummar jihar Kaduna, ina mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin tare yi masa addu'ar samun rahama."

- Uba Sani

Kaduna: An yabawa marigayin game da halayensa

Basaraken mai shekaru 87 wanda aka bayyana da mutum mai son jama'a da kuma ci gaban yankinsa ya rasu ne bayan fama da jinya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa basaraken ya kasance mai son ci gaban al'umma da kuma zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: Sarkin Kano na 15 ya rubuta takarda ga ƴan sanda kan hawan sallah

Kotu ta dawo da basarake a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa kotu ta dawo da basaraken da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya tuge a jihar.

Tsohon gwamnan ya dauki wannan matakin ne lokacin da ya ke jagorantar jihar ana saura kwanaki bakwai ya bar kujerar mulkin jihar.

El-Rufai ya cire Sarkin ne bayan barkewar wani rikici da ya yi ajalin wasu mutane da ake zargin akwai sakacin basaraken.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.