Hajji 2024: Za a Fassara Huɗubar Arafah Zuwa Hausa da Wasu Harsuna 19 Na Duniya
- Hukumar kula Masallatai masu alfarma a ƙasa mai tsarki ta ce za a fassara hudubar hawan Arfah zuwa harshen Hausa da wasu harsuna 19
- Alhazai sama da miliyan 1.5 ne za su taru a filin Arafah ranar Asabar, 16 ga watan Yuni cikinsu har da Musulmi 65,000 daga Najeriya
- Wannan rana tana da matuƙar muhimmanci da falala a addinin Musulunci kuma ana kiranta da ranar tuba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Rahotanni sun tabbatar da cewa za a fassara huɗubar hawan Arafah ta aikin hajjin bana 2024 zuwa harsuna 20 cikin har da harshen Hausa.
Ana sa ran aƙalla mutane biliyan ɗaya ne a faɗin duniya za su saurari huɗubar a Hausa da wasu harsuna 19.
Sama da mahajjata miliyan 1.5 daga sassan duniya ne ake sa ran za su taru a dutsen Arafah, wanda ya ƙunshi musulmin Najeriya 65,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar kula da manyan Masallatai biyu masu alfarma ce ta bayyana haka a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.
Shugaban hukumar, Sheikh Abdulrahman bin Abdulaziz Al-Sudais, ya ce muhimman sakonnin da huɗubar ta ƙunsa sun haɗa da juriyar addini da zaman lafiya.
Ahmed Al-Hamidi, mataimakin shugaban sashin harsuna da fassara, ya ce fassarar ta yi daidai da tsare-tsaren hukumar na shekarar 2024.
Harsuna 20 da za a fasara huɗubar Arafah
Ya ce za a fassara huɗubar zuwa Faransanci, Turanci, Farisa, Urdu, Hausa, Rashanci, Turkish, Punjabi, Chinese, Malay, Swahili, Sipaniya da Fotigal.
Sauran harsunan sune Amhari, Jamus, Sweden, Italiyanci, Malayalam, Bosniya da kuma Filipino.
Ya ce shafin Manarat Al-Haramain, tashoshi na Alqur’ani da Sunnar Annabi (SAaw) da gidajen rediyon FM guda 10 ne za su haska huɗubar kai tsaye.
Kaɗan daga falalar Arafah
Ranar hawan Arafah tana da matuƙar muhimmanci a wurin Musulmi. Ana kiran wannna rana da, "ranar tuba," saboda yadda Allah SWT ke gafartawa bayinsa matukar sun roƙe shi a ranar Arafah.
Haka nan kuma ranar tana da falala mai yawa saboda Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW) ya yi huɗubar bankwana a dutsen Arafah.
Ranar Arafah dai na zuwa ne kwana ɗaya gabanin ranar Idin layya watau Babbar Sallah kuma ita ce rana ta biyu a aikin Hajji.
Saudiyya ta tsaurara matakan tsaro
Wani rahoto ya zo cewa Kasar Saudiyya ta sanar da kammala shirye-shiryen samar da isasshen tsaro domin kare mahajjata a yayin gudanar da Hajjin bana
Ministan harkokin cikin gida, Abdulaziz bin Saud ne ya tabbatar da haka yayin wani atisaye da jami'an tsaron kasar suka gudanar
Asali: Legit.ng