Bankin Duniya: Bayan Runtumo Bashin $2.25bn, Tinubu Ya Kuma Neman Rancen $500m

Bankin Duniya: Bayan Runtumo Bashin $2.25bn, Tinubu Ya Kuma Neman Rancen $500m

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta garzaya Bankin Duniya inda ta ke neman rancen dala miliyan 500 domin gina tituna a karkara
  • Ma'aikatar noma da raya karkara ta tarayya ce ta nemi a ciyo bashin domin aiwatar da shirin RAAMP-SU wanda zai lashe dala miliyan 600
  • Wannan na zuwa ne bayan da Bankin Duniya ya amince zai ba Najeriya tallafin bashin dala biliyan 2.25 domin bunkasa tattalin arzikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Najeriya na neman rancen dala miliyan 500 daga Bankin Duniya domin gina hanyoyin karkara da kuma bunkasa kasuwancin noma a fadin kasar.

Ana sa ran kudin zai magance matsananciyar bukatar samar da ingantattun hanyoyi a yankunan karkarar, inda mutane miliyan 92 ke fama da rashin hanyoyi masu kyau.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kirkiro shirin musamman ga matasa masu hidimar NYSC

Najeriya ne neman rancen $500m daga Bankin Duniya
Tinubu ya mika kokon bara ga Bankin Duniya, yana neman rancen $500m. Hoto: @officialABAT
Asali: UGC

Manufar aiwatar da shirin RAAMP-SU

Wannan bukata na kunshe ne a cikin daftarin karshe na shirin RAAMP-SU wanda ma’aikatar aikin gona da raya karkara ta tarayya ta aiwatar kamar yadda rahoton Channels ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin RAAMP-SU yana da nufin gina hanyoyin shiga karkara masu karfin jure sauyin yanayi, ta yadda za a inganta aikin noma da kuma saukakawa manoma zuwa kasuwannin birni.

Haka zalika, ana sa ran shirin RAAMP-SU zai zama kamar wani tubali na samar da kudaden shiga da kuma dorewar titunan birane da karkara a fadin kasar.

Najeriya na neman $500m daga Bankin Duniya

An fitar da tsarin RAAMP-SU daga wani shirin samar da hanyoyi da kasuwancin noma a yankunan karkara wanda ya samu tallafi daga Bankin Duniya da hukumar raya kasar Faransa.

Ofishin raya karkara da ke karkashin ma’aikatar aikin gona da raya karkara ta tarayya ce ke jagorantar shirin, tare da sa ido daga hukumar kula da ayyukan gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta gano halin da miliyoyin dalibai ke ciki bayan an saida makarantu

An kiyasta cewa za a kashe jimillar dala miliyan 600 domin aiwatar da shirin RAAMP-SU, inda ake sa ran bankin duniya zai samar da kashi 83.33 na kudin da ake bukata.

Bankin Duniya zai ba Najeriya rancen $2.25bn

A wani labarin, mun ruwaito cewa Bankin Duniya ya amince zai ba Najeriya tallafin bashi na dala biliyan 2.25 domin inganta tattalin arziki da kuma taimakawa talakawa

Duk da cewa ba a bayyana yadda tsarin biyan bashin zai kasance ba, amma dai gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi amfani da kudin wajen aiwatar da kasafin kudin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel