Tinubu Ya Nada 'Dan Arewa a Shirgegen Mukami a Gwamnatinsa

Tinubu Ya Nada 'Dan Arewa a Shirgegen Mukami a Gwamnatinsa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sabon naɗin muƙami a gwamnatinsa inda ya amince da naɗin sabon darakta janar na ofishin kasafin kuɗi na tarayya
  • Shugaban ƙasan ya ɗauko Tanimu Yakubu, ya ba shi wannan muƙamin wanda a baya ya taɓa riƙe muƙamin babban mai ba da shawara kan tattalin arziƙi
  • Tanimu Yakubu wanda ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan kuɗi a jihar Katsina, ya maye gurbin Mista Ben Akabueze wanda wa'adinsa ya ƙare
  • A lokaci mulkin tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar'adua ne masanin kasuwancin ya zama mai ba da shawara a kan tattalin arziki har zuwa 2010

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Tanimu Yakubu a matsayin sabon darakta janar na ofishin kasafin kuɗi na tarayya.

Kara karanta wannan

Albashi: Daga karshe Tinubu ya fadi abin da gwamnati za ta biya ma'aikata

Naɗin da shugaban ƙasan ya yiwa Tanimu Yakubu na zuwa ne bayan wa'adin Mista Ben Akabueze ya ƙare.

Tinubu ya nada darakta janar na ofishin kasafin kudi
Tinubu ya nada Tanimu Yakubu mukamin darakta janar na ofishin kasafin kudi na tarayya Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya naɗa sabon muƙami

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar wanda Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin Tanimu Yakubu a matsayin darakta janar na ofishin kasafin kuɗi na tarayya, bayan ƙarewar wa'adin Mista Ben Akabueze."
"Tanimu Yabuku ƙwararren masanin tattalin arziƙi ne wanda ya riƙe muƙamin babban mai ba da shawara kan tattalin arziƙi ga tsohon shugaban ƙasa daga shekarar 2007 zuwa 2010, tsohon shugaban bankin FMBN daga shekarar 2003 zuwa 2007."
"Ya kuma taɓa riƙe muƙamin kwamishinan kuɗi, tattalin arziƙi a jihar Katsina daga shekarar 1999 zuwa 2003."

- Ajuri Ngelale

Kara karanta wannan

Albashi: Kungiyar NLC ta juyawa Tinubu baya, ta fadi gaskiyar halin da ake ciki

Shugaba Tinubu ya godewa Darakta janar mai barin gado, Ben Akabueze bisa aikin da ya yi tare da yi masa fatan nasara a dukkanin inda rayuwa ta kai shi nan gaba.

Tinubu ya faɗi albashin da zai biya ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta amince ne kawai da sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan da za ta iya biya.

Shugaban ƙasan ya nuna cewa nan ba da jimawa ba zai aika da sabon ƙudiri kan mafi ƙarancin albashin ga majalisar dattawa ta Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel