Gwamna Ya Bada Kyautar N6m ga Iyalan Jami’an Tsaro da ’Yan Bingida Suka Kashe

Gwamna Ya Bada Kyautar N6m ga Iyalan Jami’an Tsaro da ’Yan Bingida Suka Kashe

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya bada tallafin Naira miliyan shida ga iyalan jami'an tsaro da aka kashe a makon jiya
  • Mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun kashe jami'an 'yan sanda shida da jami'an tsaron KSWC uku a harin da suka kai Kankara
  • Kowanne iyalin 'yan sandan ya samu N500,000 yayin da aka bada N1,000,000 ga kowanne iyalinn jami'an tsaron jihar guda uku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta bada kyautar Naira miliyan shida ga iyalan 'yan sanda shida da jami'an tsaron KSWC uku da aka kashe.

Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun kashe jami'an 'yan sandan da na tsaron jihar ne a yammacin ranar Lahadi a karamar hukumar Kankara ta jihar.

Kara karanta wannan

Jigon APC, Salihu Lukman ya nakasa jamiyyar bayan ya yi murabus, ya jero dalillai

Gwamnatin Katsina ta tallafawa iyalan jami'an tsaro da aka kashe
Katsina: Dikko Radda ya ba iyalan jami'an tsaron da aka kashe kyautar N6m. Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

An ba iyalan jami'an tsaro kyautar N6m

Rahoton Channels TV ya nuna cewa Gwamna Dikko Radda ya ba kowanne iyali na 'yan sandan N500,000, yayin da kowane iyali na jami'an KSWC suka samu N1,000,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar, Isah Mohammed Kankara ne ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa raba kudin.

An ce an yi rabon kudin ne a hedikwatar 'yan sandan jihar yayin da gwamnatin ta mika ta'aziyya ga rundunar da kuma iyalan wadanda aka kashe.

Gwamnati ta damu da hare-hare a Katsina

A yayin gabatar da kudin, kwamishinan ya nuna matukar damuwarsa kan yadda ake ci gaba da yin asarar rayuka a kananan hukumomin Ƙanƙara, Safana da Danmusa.

Alhaji Isah Kankara ya kuma jinjinawa jami'an da aka kashe bisa kokarinsu na yaki da 'yan bindiga, barayin shanu, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuffuka.

Kara karanta wannan

Ana dab da zabe, ‘yan sanda sun kama kakakin yakin zaben gwamnan PDP, an gano dalili

Gwamnoni su yi koyi da na Katsina

A nasa jawabin, kwamishinan 'yan sandan jihar, Abubakar Musa, ya mika godiya ga tawagar gwamnatin jihar tare da nuna muhimmancin wannan ta'aziyyar da tallafin.

Ya jaddada kudurinsa da na jami'an rundunarsa na yaki da 'yan bindiga a jihar, tare da yin kira ga gwamnonin Arewa maso Yamma da su yi koyi da Gwamna Dikko Radda.

A cewar kwamishinan, ayyukan 'yan bindiga ya ragu sosai saboda kokarin gwamnatin jihar da jami'an tsaro da kuma addu'o'i daga daukacin al'umar jihar.

'Yan bindiga sun kai hari jihar Katsina

Tun da fari, mun ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 22 da jami'an tsaro bakwai a kauyukan karamar hukumar Kankara.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abubakar Sadiq ya fitar a ranar Litinin, ya ce ‘yan bindigar sun kashe jami’an rundunar hudu da jami'an KSWC guda uku.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel