Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci a Shari'ar da Tinubu Yake Yi da Gwamnoni 36
- Kotu ta dauki mataki game da shari'ar da ake yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma gwamnonin jihohi 36 a Najeriya
- Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar inda ta bukaci duka bangarorin su saurari ranar da za ta tuntube su
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnoni a gaban kotu kan dakile ƴancin ƙananan hukumomi a kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar Gwamnatin Tarayya da gwamnonin jihohi 36 a Najeriya.
Kotun ta dauki matakin ne a yau Alhamis 13 ga watan Yuni kan korafin da aka shigar da gwamnonin kan ƴancin ƙananan hukumomi a kasar.
Matsayar kotu a shari'ar Tinubu da gwamnoni
Mai Shari'a, Mohammed Lawal Garba wanda ya jagoranci alkalan guda bakwai ya ce za su byyana ranar yanke hukuncin karshe ga duka bangarorin, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lawal Garba ya bayyana haka ne jim kadan bayan lauyoyin duka bangarorin sun gabatar da korafe-korafensu kan shari'ar, Vanguard ta tattaro.
Musabbabin ƙarar gwamnoni da Tinubu ya yi
Hakan ya biyo bayan maka gwamnoni 36 da ke Najeriya kan zargin tauye hakkin kananan hukumomi 774 da suke yi.
Daga bisani kotu ta ba gwamnoni 36 wa'adin mako daya da su yi martani kan zarginsu da ake yi.
Gwamnonin jihohi sun kalubalanci shari'ar inda suka bukaci babbar kotun da ya yi fatali da korafin Gwamnatin Tarayya a kansu.
Har ila yau, kotun ta umarci Ministan Shari'a ya yi martani cikin kwanaki biyu bayan karbar korafi daga gwamnonin.
Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnoni a kotu
A wani labarin, kun ji yadda Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta maka gwamnonin jihohin Najeriya 36 zuwa Kotun Koli.
Matakin da aka dauka na shari’a kan gwamnoni 36 ya biyo bayan rashin da’a da ake zarginsu da aikatawa a harkokin gudanar da kananan hukumomi.
Babban lauyan Tarayya kuma Ministan shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya shigar da karar mai lamba: SC/CV/343/2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng