Yahaya Bello: EFCC Ta Fadi Dalilin Kasa Cafke Tsohon Gwamna Kan Badakalar N80bn
- Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC, ta bayyana dalilin da ya sa ta kasa kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello
- Hukumar ta ce wasu manya ne ke ba tsohon gwamnan kariya kan zargin da ake masa na badaƙalar N80.2bn a lokacin da yake gwamna
- Muƙaddashin daraktan hukumar EFCC na shiyyar Benin, Effa Okim, wanda ya bayyana hakan ya ce Yahaya Bello ya kunyata tsarin shari’ar Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta faɗi dalilin kasa cafke tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
EFCC ta ce ta kasa cafke Yahaya Bello ne saboda akwai manyan da suke ba shi kariya.
Meyasa EFCC ta kasa cafke Yahaya Bello?
Muƙaddashin daraktan hukumar EFCC na shiyyar Benin, Effa Okim, ya ce Yahaya Bello, wanda ake zargi kan badaƙalar N80.2bn yana samun kariya daga manya, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Effa Okim ya bayyana haka ne a wata ziyara da ya kaiwa ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Delta a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, rahoton jaridar PM News ya tabbatar da hakan.
Ya ce abin kunya ne ga tarayyar Najeriya cewa har yanzu ba a kama Yahaya Bello ba, makonni bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.
EFCC ta fusata kan Yahaya Bello
Daraktan na hukumar ta EFCC ya nuna cewa tsohon gwamnan ya kunyata tsarin shari'ar Najeriya saboda rashin gabatar da kansa a gaban kotu.
"Yahaya Bello wanda aka gano laifinsa EFCC ta gayyace shi ya zo ya yi bayani, amma tsawon watanni yana wasan ɓuya. Wannan abin kunya ne a garemu."
"Shin ba za mu iya kama shi ba? Za mu iya amma mun yi ƙoƙarin yin hakan? Muna buƙatar yin hakan bayan yana da iyayen gidansa?"
"Shin ba za su iya kiransa su gaya masa cewa kana kunyata Najeriya ba? Me yake nunawa duniya? Su gaya masa ya kai kansa ya yi bayani kamar yadda saura suka yi."
- Effa Okim
Yahaya Bello zai kansa kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello zai gurfana a gaban kotu makonni bayan hukumar EFCC ta bayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.
Yahaya Bello zai kai kansa babbar kotun tarayya da ke Abuja bayan ya daɗe yana wasan ɓuya da hukumar EFCC kan zargin badakalar N80bn lokacin da yake kan mulkin jihar Kogi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng