"Ka Bi Sawun Kakanka," Iyalan Sheikh Ibrahim Nyass Sun Aike da Sako Ga Sanusi II
- Iyalan Sheikh Nyass sun bayyana matsayarsu kan rigimar sarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero
- A wata sanarwa da Sheikh Muhammad Mahy Ibrahim Nyass ya fitar sun roƙi Sanusi II ya bi sahun kakansa, kada ya koma kujerar sarki
- Wannan na zuwa ne yayin da babbar kotun tarayya mai zama a Kano ke shirin yanke hukunci kan hurumin sauraron ƙarar masarauta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Iyalan fitaccen shehun malamin nan, Sheikh Ibrahim Nyass, sun buƙaci sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bi sawun kakansa kar ya koma sarauta.
Iyalan Nyass sun roƙi Sanusi II, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya yi koyi da kakansa, Sanusi I wanda ya ƙi karɓan tayin mayar da shi kan sarauta.
Sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da suka turawa jaridar Daily Trust a jihar Kano a daidai lokacin da ake ci gaba da taƙaddama kan karagar sarkin Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma iyalan Nyass sun roki Sanusi II ya ba sha'anin zaman lafiyar jihar muhimmanci ta hanyar haƙura da sarauta, ya ajiye rawanin da aka sake naɗa masa.
Iyalan Nyass sun magantu kan sarautar Kano
A cikin sanarwar mai dauke da sa hannun Sheikh Muhammad Mahy Ibrahim Nyass, iyalan sun ce:
"Mu iyalan Shehin Musulunci Gausuz-zaman, Sheikh Ibrahim Nyass na Kaulaha, Senegal, muna ganin ya kamata mu yi magana kan abubuwan da ke faruwa a masarautar Kano.
"Muna alfahari da jihar Kano kasancewarta cibiyar ƴan uwa mabiya Ɗarikar Tijjaniya a Najeriya.
"Mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamma Abba Kabir Yusuf ta yi ya haifar da damuwa da fargaba."
A cewarsu, ya kamata mai martaba sarkin ya fifita batun zaman lafiya fiye da abin da ransa ke so na dawowa kan sarautar da ya rasa shekarun da suka gabata.
An nemi Sanusi II ya haƙura da sarauta
A rahoton Premium Times, sun kara da cewa:
"Ba za mu manta da jagorancin marigayi Muhammadu Sanusi I ba wanda ya ƙi yarda ya koma kan kujerar sarki bayan tsige shi."
"Don haka muna kira ga Khalifa Muhammad Sanusi da ya bi sahun kakansa ya ba da fifiko ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin Kano."
An shirya yanke hukunci kan sarautar Kano
Rahoto ya zo mana cewa babbar kotun tarayya za ta yanke hukunci kan ko tana da hurumin sauraron shari'ar sarautar Kano a yau Alhamis, 13 ga watan Yuni.
Aminu Babba Ɗanagundi ne ya kai ƙara gaban kotun yana ƙalubalantar matakin gwamnatin Kano na mayar da Sarki Sanusi II.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng