'Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Kaduna Zuwa Abuja, Sun Sace Fasinjoji Masu Yawa

'Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Kaduna Zuwa Abuja, Sun Sace Fasinjoji Masu Yawa

  • Ƴan bindiga sun tafka ta'asa a jihar Kaduna bayan sun tare titin hanyar Kaduna zuwa Abuja a cikin dare
  • Miyagun sun fasa tayar wata mota mai ɗauke da fasinjoji 18 sannan suka tasa ƙeyarsu zuwa cikin daji a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar
  • Ƴan bindigan ɗauke da makamai sun kuma yi awon gaba da fasinjojin wasu motoci guda biyu yayin da suka ci karensu babu babbaka a kan hanyar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji da dama bayan sun buɗe wuta kan wata motar bas mai ɗauke da mutum 18 a kan titin hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ƴan bindigan sun buɗe wuta kan motar ne a mahaɗar Bishini, kusa da Katari a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun mayar da martani, sun halaka ƴan bindiga da yawa a Arewa

'Yan bindiga sun sace mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja
'Yan bindiga sun sace fasinjoji a hanyar Kaduna zuwa Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Yadda ƴan bindiga suka sace fasinjoji

Wani mazaunin Katari mai suna Saleh Ibrahim ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Litinin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saleh Ibrahim ya ce ƴan bindigan sun fito daga daji ne a wata lanƙwasa sannan suka buɗe wuta kan motar bas ɗin da ke jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna.

Ya ce ƴan bindigar sun harbi tayoyin motar bas ɗin wanda hakan ya tilastawa motar ta kauce daga kan hanyar zuwa cikin daji, kafin daga bisani suka tasa dukkanin fasinjojin zuwa cikin daji.

Ya kuma ƙara da cewa, ƴan bindigan sun yi awon gaba da fasinjojin wasu motoci guda biyu.

"Babban abin ban haushi shi ne, wurin da lamarin ya faru tun daga mahaɗar Bishini zuwa inda sojoji suka sanya shingen bincikensu bai wuce kilomita ɗaya ba."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ɓarna, sun tafi da matafiya da yawa a hanyar zuwa Abuja

- Saleh Ibrahim

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba ta ce komai ba kan sace fasinjojin da ƴan bindiga suka yi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Hassan Mansur, domin samun ƙarin bayani, sai dai bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan bindiga sun kai hari a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutum 22 a ƙauyukan Gidan Bofa da 'Dan Nakwabo a ƙaramar hukumar Kankara ta jihar.

Ƴan bindigan sun kuma kashe jami’an ƴan sanda mutum huɗu da suka haɗa da sufeto uku da kofur ɗaya tare kashe wasu jami'an rundunar KSWC mutum biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel