"Ba Faɗuwa Na Yi Ba" Bola Tinubu Ya Yi Magana Kan Abin da Ya Faru a Eagle Square

"Ba Faɗuwa Na Yi Ba" Bola Tinubu Ya Yi Magana Kan Abin da Ya Faru a Eagle Square

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi magana a karon farko kan zamewar da ya yi ya faɗi a lokacin hawa motar fareti a birnin tarayya Abuja
  • Shugaban ƙasar ya bayyana cewa shi ɗan yarbawa ne, wannan abin da aka gani rusunawa ya yi a al'adarsu wanda ake kira da dobale
  • Faɗuwar Tinubu yayin da zai hau motar da za ta zagaya da shi ya kalli faretin sojoji a Eagle Square ta haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan zamewar da ya yi har ya faɗi ƙasa a lokacin da zai hau mota a filin Eagle Square ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Albashi: Daga karshe Tinubu ya fadi abin da gwamnati za ta biya ma'aikata

Idan ba ku manta ba Legit Hausa ta kawo muku rahoton yadda Tinubu ya zame a lokacin da yake ƙoƙarin hawa motar faretin bikin ranar dimokuraɗiyya.

Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu ya ce faɗuwar da ya yi ba wani abin damuwa ba ne domin duk cikin murna ne Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Bayan faruwar lamarin, kafafen sada zumunta suka hargitse da mayar da martani, inda mutane suka riƙa tofa albarkacin bakinsu kan faɗuwar Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya faɗi abin da ya jawo faɗuwarsa

Yayin da yake tsokaci kan lamarin a wurin liyafar cin abinci da aka shirya, Shugaba Tinubu ya ayyana faɗuwar a matsayin wani salon suwaga, Daily Trust ta ruwaito.

A rahoton Channels tv, Bola Tinubu ya ce ba faɗuwa ya yi ba, rusunawa ya yi domin girmama ranar dimokuraɗiyya a al'adar Yarbawa.

Ya ce:

"Da safiyar yau, na gamu da wani tsautsayi kuma nan take ya mamaye soshiyal midiya, sun rikice sun gaza gane ko 'buga' na yi ko 'babbaringa'.

Kara karanta wannan

"Yar zamewa kawai ya yi," fadar shugaban kasa ta yi bayanin faduwar Bola Tinubu

"Amma ku tuna rana ce ta murnar dimokuraɗiyya, muna rusunawa a al'adar dobale. Ni ɗan yarbawa ne saboda haka na rusuna ne kawai."

Fadar shugaban ƙasa ta magantu

Tun farko dai fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani kan abin da ya faru, inda ta bayyana cewa Bola Tinubu mutum ne kamar kowa da tsautsayi ka iya afka masa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya jajantawa Tinubu sakamakon faɗuwar ya yi a wurin faretin sojoji na ranar dimokuraɗiyya.

Jerin shugabannin da suka taɓa faɗuwa

Kuna da labarin bayan Bola Tinubu, akwai wasu shugabannin kasashen duniya da suka taba faduwa yayin hawa jirgi ko abin hawa.

Legit Hausa ta jero muku shugabannin kasashen da suka gamu da tsautsayin a kokarin sauka ko hawa matakala kamar yadda ya faru da shugaban Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262