'Yan Daba Sun Tada Hargitsi a Kano Yayin da Ake Tsaka da Rikicin Sarauta
- Ƴan daba sun tayar da hargitsi a kasuwar da ke Masallacin idi a Kano bayan gwamnatin jihar ta umarci mutane su tashi
- Gwamnatin Kano ta bai wa ƴan kasuwar wa'adin sa'o'i 48 su tashi daga wurin, amma har yanzu ana ci gaba da hada-hada
- Ɗaya daga cikin ƴan kasuwar ya buƙaci gwamnati ta sake tunani domin sama da shekara 10 da suka wuce aka ba su wurin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Wasu fusatattun ƴan daba sun tayar da hargitsi a kasuwar filin masallacin idi da ke cikin birnin jihar Kano ranar Laraba yayin da ake shirye-shiryen Babbar Sallah.
Wannan ya biyo bayan wa'adin sa'o'i 48 da gwamnatin jihar Kano ta bai wa ƴan kasuwar su tattara kayansu su tashi daga filin.
KNUPDA ta tashi 'yan kasuwan Kano
Hukumar kula da tsare-tsare da raya birane ta jihar Kano (KNUPDA) ce ta bayar da wannan umarni na tashin ƴan kasuwar da suka jima suna neman halak a wurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta kuma yi gargaɗin cewa duk wanda ya yi kunnen ƙashi za a ɗauki mataki a kansa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Duk da cewa wa’adin tashin da gwamnati ta bayar ya cika, ‘yan kasuwa sun ci gaba da harkokinsu na kasuwanci a kasuwar masallacin idin.
Sai dai alamu sun nuna akwai damuwa da fargabar matakin da gwamnati za ta ɗauka a fuskokin ƙananun ƴan kasuwa 5,000 da ke kusa da filin idin.
Kasuwar ta haura shekara 10 a Kano
Daya daga cikin ‘yan kasuwar, Abdullahi Baba, wanda ya zanta da gidan talabijin ya bayyana damuwarsa kan wa’adin sa’o’i 48 da gwamnati ta bayar a tashi.
"An bamu wannan wurin tun shekara 10 da ya wuce, kasuwancin da muke yi ya taimaka wajen rage satar waya, sace-sace da sauran laifuffuka, to me ya kawo wannan?"
"Ya kamata gwamnati ta sake tunani kan matakin tashinmu, bam u da wata hanyar samun na sawa a bakin salati,"
- Abdullahi Baba
Tuni dai aka tura jami'an ƴan sanda da ƴan KAROTA wurin kuma sun samu nasarar dawo da zaman lafiya da kwnaciyar hankali.
Sanusi Isiyaku, wani ɗan Kwankwasiyya a Kano ya ce a duk lokacin da za a yi gyara dole wasu za su sha wahala wasu kuma abin zai ƙaro masu ci gaba.
Da yake zantawa da wakilin Legit Hausa, ya ce tashin ƴan kasuwa a filin idi ci gaba ne a wurin mu saboda wurin na gwamnati ne amma tabbas za a kashe hannyar cin abincin mutane.
"Lamarin fa akwai matsala, amma ni na fi ganin da gwamnati za ta taimaka ta samar masu wani wurin su koma can, saboda gaskiya suj daɗe suna zama a wurin.
"Babu shakka wurin gwamnati ne to amma dai idan aka ɗauki wannan matakin za a naƙasa wasu, muna fatan mahukunta su sake nazari," in ji shi.
Sarki Aminu ya fara shirin hawan Sallah
A wani rahoton na daban, an ji yayin da ake ci gaba da rigimar sauratar Kano, ta tabbata Aminu Ado Bayero zai yi hawa domin bukukuwan sallah.
Sarki na 15, Aminu Ado ya rubuta takarda ta musamman ga jami'an 'yan sanda domin samar da tsaro ga al'ummar jihar Kano yayin bukukuwan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng