Jerin Ranakun da Musulmai Za Su Yi Hutu a Watannin Yuni/Yulin 2024

Jerin Ranakun da Musulmai Za Su Yi Hutu a Watannin Yuni/Yulin 2024

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar ya ayyana ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, a matsayin ranar Idin babbar Sallah
  • A nan gaba kaɗan Sarkin Musulmi zai ayyana ranar, 1 ga Muharram, 1446 bayan Hijira a matsayin wata na farko na kalandar Musulunci
  • A saboda haka wasu jihohin Najeriya za su ayyana hutun domin murnar shiga sabuwar shekara ta addinin Musulunci da za ta zo a watan Yuli

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu a Najeriya.

An sanar da ranar a matsayin ranar da babu aiki domin tunawa da ranar dimokuradiyya ta shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Ranar dimokuradiyya: Gwamnatin tarayya ta ba ƴan Najeriya hutun kwana 1

Hutun Musulmai za su yi a Yuni/Yuli 2024
Za a yi hutun babbar Sallah a watan Yunin 2024 Hoto: Majority World
Asali: Getty Images

Baya ga wannan hutun gama-garin da za a yi a Najeriya, akwai aƙalla hutu guda biyu da mabiya addinin Musulunci za su yi a watan Yuni da Yuli na shekarar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga ranakun a nan ƙasa:

1) Eid el-Kabir (Babbar Sallah) 2024

Nan gaba kaɗan a cikin wannan watan na Yuni, gwamnatin tarayya za ta ayyana aƙalla hutun kwanaki biyu domin hutun bikin babbar Sallah.

Ma'aikatar cikin gida za ta fitar da sanarwar. Bikin babbar Sallah na da matuƙar muhimmanci ga al'ummar musulmi.

A lokacin bikin babbar Sallah, al'ummar Musulmai suna gudanar da ibadar layyah domin samun lada a wajen Allah maɗaukakin Sarki.

2) 1 ga watan Muharram 1446

Gwamnatocin jihohi irinsu Kebbi, Sokoto, Kwara suna ayyaɓa ranar 1 ga watan Muharram na shekarar Musulunci a matsayin ranakun hutu.

Kara karanta wannan

Bankin CBN ya soke lasisin wasu manyan bankuna 4 a Najeriya? Gaskiya ta fito

A yanzu al'ummar Musulmi na cikin shekara ta 1445 bayan Hijirar Annabi Muhammad (SAW).

Watan Muharram na shekarar 1446 bayan Hijira (sabuwar shekara) zai fara ne a cikin watan Yulin 2024.

Saboda hakan wasu jihohi za su sanar da ranar hutu domin shigowar sabuwar shekarar musulunci.

Sarkin Musulmi ya sanar da ranar Sallah

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya sanar da cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah a Najeriya da yammacin ranar Alhamis.

Sarkin Musulmin kuma shugaban majalisar ƙoli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ce ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuni ta zama 1 ga watan Dhul Hijjah, 1445H.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel