Gwamna Ya Bayyana Rufa Rufar da Ake Yiwa Tinubu Kan Rashin Tsaro

Gwamna Ya Bayyana Rufa Rufar da Ake Yiwa Tinubu Kan Rashin Tsaro

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a jihar da yankin Arewacin Najeriya
  • Gwamnan ya bayyana cewa ba a sanar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu haƙiƙanin halin da ake ciki dangane da matsalar rashin tsaro
  • Ya bayyana cewa idan gwamnati da gaske take yi, za a iya kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a cikin mako biyu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana cewa ba a gayawa Shugaba Bola Tinubu cikakkun bayanai kan matsalar rashin tsaro.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa akwai siyasa dangane da matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya fadi amfanin da Zamfara ta samu silar zaman Matawalle ministan tsaro

Gwamna Dauda ya magantu kan rashin tsaro
Gwamna Dauda Lawal ya ce ba a sanar da Tinubu halin da ake ciki kan rashin tsaro Hoto: Dauda Lawal, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana cewa idan har gwamnati da gaske take yi, za a iya kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro cikin mako biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Sunrise Daily'.

Me Gwamna Dauda ya ce kan Tinubu?

Da yake amsa tambaya kan ko yana tunanin Shugaba Tinubu na samun bayanai kan matsalar rashin tsaron, Gwamna Dauda ya ce baya tunanin ana gaya masa haƙiƙanin halin da ake ciki.

"Bisa ga tattaunawar da muka yi da shi, amsar ita ce a'a. Sai da na yi masa bayanin komai, abin da muke fama da shi da abin da ake da buƙatar a yi."
"Jihar Zamfara ta zama matattarar ƴan bindiga a Arewacin Najeriya. Idan za a kawo ƙarshen matsalar a yau a Zamfara, na yi amanna cewa za a magance kaso 90% na matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya."

Kara karanta wannan

Gwamna ya nuna adawa da kafa 'yan sandan jihohi, ya fadi dalilansa

"Idan muka nuna jajircewa, muka nuna da gaske muke, za mu iya shawo kan matsalar cikin mako biyu kacal. Amma babu niyyar yin hakan."

- Dauda Lawal

Gwamna Dauda ya caccaki Matawalle

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi magana kan amfanin da jihar ta samu sakamakon zaman Bello Matawalle ƙaramin ministan tsaro.

Gwamnan ya bayyana cewa jihar Zamfara ba ta amfana da komai ba sakamakom zaman tsohon gwamnan ƙaramin ministan tsaro a gwamnatin Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel