Fadar Shugaban Kasa ta Fadi Ranar da Shugaba Tinubu zai Yiwa 'yan Najeriya Jawabi
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga 'yan Najeriya yayin da ake bikin dimukuradiyya ranar Laraba
- Mashawarcin shugaban kasa kan kafafen yada labarai, Cif Ajuri Ngalale ne ya sanar da haka a yau, inda ya ce shugaban zai yi jawabi ta manyan kafafen yada labarai
- A gobe Laraba ne za a yi bikin ranar dimukuradiyya da tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya sauya zuwa 12 ga watan Yuni domin martaba MKO Abiola
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Yayin da ake shirin bikin ranar dimukuradiyya a gobe Laraba, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yiwa 'yan kasa jawabi.
Mashawarcin shugaban kasa na musamman kan yada labarai, Cif Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a sanarwar da ya fitar yau Talata.
Mista Ngelale ta sakon da ya wallafa a shafinsa na facebook ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu zai yi jawabin da za a watsa a kafafen yada labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu zai yi bayani da safe
Da misalin 7:00 na safiyar gobe Laraba ne ake sa ran shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga 'yan Najeriya a wani bangare na bikin ranar dimukuradiyya kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
Mashawarcin shugaba Tinubu kan kafafen yada labarai, Ajuri Ngalale ya ce za a yada jawabin shugaban kasar a tashar talabijin ta NTA da radiyon tarayya ta FRCN.
Tun a shekarar 2018 tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya ranar dimukuradiyyar kasar nan daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 Yuni domin martaba MKO Abiola.
Ranar dimukuradiyya: An bayar da hutu
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ba 'yan Najeriya hutun kwana daya a wani bangare na bikin ranar dimukuradiyya a gobe Laraba.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar, inda ya bukaci 'yan Najeriya su rika yaba kokarin da shugaba Tinubu ke yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng