Bola Tinubu Ya Tsige Shugaban Hukumar PSC, Ya Maye Gurbinsa da Ɗan Arewa

Bola Tinubu Ya Tsige Shugaban Hukumar PSC, Ya Maye Gurbinsa da Ɗan Arewa

  • Bola Ahmed Tinubu ya sauke Solomon Arase daga matsayin shugaban hukumar jin daɗin ƴan sanda ta ƙasa (PSC) ranar Litinin, 10 ga watan Yuni
  • Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya ce Tinubu ya naɗa DIG Hashimu Argungu a matsayin wanda zai maye gurbin
  • Hat ila yau Mai girma Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Mohammed Sheidu a matsayin babban sakataren hukumar NPTF

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Solomon Arase a matsayin shugaban hukumar jin daɗin ‘yan sanda (PSC) ta kasa.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ne ya bayyana wannan sauyin da aka samu a wata sanarwa da ya fitar ranar Litini.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta yanke hukunci kan tsige ƴan majalisa 27 da suka sauya sheƙa zuwa APC

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauye a hukumar jin daɗin ƴan sanda ta ƙasa Hoto: DOlusegun
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya naɗa sabon shugaban PSC

Ya ce DIG Hashimu Argungu (mai ritaya) shi ne sabon shugaban hukumar jin dadin ƴan sanda, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya kuma amince da nadin Cif Onyemuche Nnamani a matsayin Sakataren PSC da DIG Taiwo Lakanu (mai ritaya) a matsayin mamban gudanarwa.

"Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin DIG Hashimu Argungu (Rtd) a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC).
"Shugaban ƙasar ya kuma amince da nadin Cif Onyemuche Nnamani a matsayin Sakataren hukumar da DIG Taiwo Lakanu (Rtd) a matsayin mamba gudanarwa.
"Naɗin zai tabbata ne bisa sahalewar majalisar dattawa. Haka nan kuma shugaban zai nada sauran mambobin gudanarwa na PSC nan gaba kaɗan."

- Ajuri Ngelale.

Shugaba Tinubu ya naɗa shugaban NPTF

Bugu da kari, Bola Tinubu ya naɗa Mista Mohammed Sheidu a matsayin babban sakataren asusun rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPTF) ba tare da bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Sallah: Bayan Sanata Yari, ɗan Majalisa ya ba ƴan mazaɓa raguna 300, N250m a Zamfara

Tinubu ya yi fatan cewa waɗanda aka nada zasu nuna gaskiya, kwazo, da kishin kasa wajen gudanar da muhimman ayyukan da suka rataya a wuyansu.

A cewarsa, hakan ne zai kawo ci gaban ayyukan ƴan sanda da kuma ƙasar nan baki ɗaya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

CBN ya musanta soke lasisin bankuna 4

A wani rahoton kuma, Bankin CBN ya musanta rahoton da ke yawo cewa yana shirin soke lasisin bankunan Fidelity, Polaris, Wema da kuma Unity.

Muƙaddashiyar kakakin CBN, Hakama Sidi Ali, ta yi ƙarin haske kan takardar da ke yawo a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, 10 ga watan Yuni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262