'Yan Bindiga Sun Yi Aika Aika a Imo, Sun Kashe 'Yan Sanda da Farar Hula

'Yan Bindiga Sun Yi Aika Aika a Imo, Sun Kashe 'Yan Sanda da Farar Hula

  • A safiyar yau talata, 11 ga watan Yuni wasu yan bindiga suka afkawa jami'an yan sanda da suke bakin aiki a jihar Imo
  • Shaidar gani da ido ya tabbatarwa manema labarai cewa yan bindigar sun kashe wasu jami'an tsaro da farar hula yayin harin
  • Har ila yau, wanda ya shaida lamarin ya kara da cewa harin ya tayar da hankulan mazauna yankin inda ake zaman ɗar-ɗar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Imo - An wayi gari cikin ɗar-ɗar yayin da wasu yan bindiga suka kai hari kan jami'an tsaro a jihar Imo.

Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun kai hari ne kan jami'an yan sanda yayin da suke cikin aiki.

Kara karanta wannan

Ana daf da gudanar da zabe, 'yan bindiga sun harbe jigon dan takarar PDP

Police
An kashe yan sanda 2 a jihar Imo. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an kai harin ne a daidai hanyar Ama-John da ke Okigwe a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe yan sanda a Imo

Mazauna yankin sun tabbatar da cewa yan bindigar sun yi kwanton ɓauna ne a safiyar yau suka afka kan jami'an yan sanda.

Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun yi nasarar kashe yan sanda biyu da wani farar hula daya yayin harin.

Yanayin gari bayan kashe 'yan sanda

Wani mutum da ya shaida lamarin yace a yanzu haka mutane sun watse a wurin da aka kai harin, rahoton the Cable.

Mutumin ya ce duk da kasancewar wurin ana hada-hada sosai amma ko masu abubuwan hawa sun taƙaita bin hanyar.

Yan sanda ba su ce komai ba

Yayin da aka tuntubi yan sandan jihar, kakakin rundunar, Henry Okoye ya ce bai samu karin haske ba a lokacin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a Arewa, sun kashe yan sanda da mutane da asuba

Yan bindigar su hudu sun kai harin ne a cikin wata mota kirar Sienna Toyota kuma sun arce bayan aikata ta'addancin.

Kwastam ta kama masu safarar mai

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an hukumar kwastam sun kama masu safarar mai a iyakokin Najeriya daga sassa daban-daban na kasar.

Shugaban hukumar, Bashir Adewale Adeniyi ya bayyana adadin man fetur da suka kwato da kuma yadda masu safarar ke barazana ga tsaron kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng