Wike Na Cikin Alheri Dumu Dumu: Majalisa Ta Amince da Karin N98.5bn a Kasafin Abuja

Wike Na Cikin Alheri Dumu Dumu: Majalisa Ta Amince da Karin N98.5bn a Kasafin Abuja

  • Majalisar dattawa ta amince da bukatar gwamnatin tarayya na ƙara Naira biliyan 98.5 a cikin kasafin kudin babban birnin tarayya
  • A makon da ya gabata ne majalisar wakilai ta amince da kudirin wanda aka gabatar wa majalisar dattawa domin ita ma ta amince
  • Shugaba Bola Tinubu ya shaidawa majalisun tarayyar cewa karin kudin zai taimaka wajen kammala wasu muhimman ayyuka a Abuja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Majalisar dattijai ta amince da karin Naira biliyan 98.5 a kasafin shekarar 2024 na ma'aikatar kula da babban birnin tarayya, Abuja.

Majalisar dattawan Najeriya
Majalisar dattawa ta amince a kara wa babban birnin tarayya kudi a kasafin 2024. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Abuja ya samu karin kasafin kudi

Jaridar This Day ta ce a makon da ya gabata majalisar wakilai ta fara amince wa da kudurin dokar gabanin gabatar da shi ga majalisar dattawan.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa na neman mayar da ofishin mataimakin shugaban ƙasar Najeriya ya zama 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya bayyana amincewa da kudurin karin kudin a zaman majalisar na yau, kamar yadda rahoton Channels ya nuna.

Majalisar ta amince da kudirin dokar ne bayan duba rahoton da kwamitin ta na babban birnin tarayya ya gabatar mata kan karin kasafin kudin.

'Yar majalisa ta gabatar da korafi

Kafin amincewa da rahoton, Sanata Ireti Kingibe, ta gabatar da wani korafi na cewa an yi watsi da ita a ayyukan kwamitin na babban birnin tarayya duk da ta kasance mamba a ciki.

Shugaban majalisar dattawan ya duba korafin nata inda ya ba ta shawarar da ta bi ka’ida, ta hanyar rubuta kokenta, ta gabatar shi a gaban majalisar a matsayin kudiri.

Sakon Tinubu ga majalisa kan kasafin Abuja

Legit Hausa ta ruwaito cewa a kwanakin baya ne shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar da kudirin karin kasafin kudin birnin tarayyar a gaban majalisar tarayyar.

Kara karanta wannan

Kudurin ƙirƙirar sabuwar jiha a Kudu maso Gabas ya wuce karatun na 1 a majalisar wakilai

Tinubu ya tunatar da ‘yan majalisar cewa ana bukatar kudin ne domin gudanar da muhimman ayyukan more rayuwa a babban birnin kasar wanda ba ya a cikin kasafin na farko.

Majalisa na neman sauya tsarin mulki

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan majalisar wakilai sun gabatar da kuduri da zai taikata wa'adin shugaban kasa da gwamnoni zuwa shekara shida babu tazarce.

Haka zalika kudurin na neman a kirkiri karin ofishin mataimakin shugaban kasa ta yadda shiyyoyin Arewa da Kudu za su zamo suna da kujerar mataimaki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel