"Yan Bindiga Sun Shiga Uku," Gwamna Ya Sha Alwashin Dawo da Zaman Lafiya Duk Runtsi

"Yan Bindiga Sun Shiga Uku," Gwamna Ya Sha Alwashin Dawo da Zaman Lafiya Duk Runtsi

  • Malam Dikko Umaru Radɗa ya sha alwashin kawo ƙarshen ƴan bindiga gaba ɗaya a jihar Katsina biyo bayan harin Kankara
  • A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ƴan bindiga suka kai hari kauyen Gidan Boka, suka kashe mutane kusan 30 ciki har da jami'an tsaro
  • Da yake jajantawa waɗanda harin ya shafa, Gwamna Radda ya ce gwamnatinsa ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen dawo da tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗda ya sha alwashin kawo karshen ƴan bindiga domin a samu zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya yi wannan alƙawari ne biyo bayan mummunan harin da aka kai kan bayin Allah a kauyen Gidan Boka, ƙaramar hukumar Kanƙara a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Gwamna ya nuna adawa da kafa 'yan sandan jihohi, ya fadi dalilansa

Gwamna Dikko Radda na Katsina.
Malam Dikko Radda ya sha alwashin kawar da ƴan bindiga a jihar Katsina Hoto: Isah Miqdad
Asali: Facebook

Harin da ƴan bindiga suka kai ranar Lahadi, 9 ga watan Yuni, 2024, da misalin karfe 3:00 na yamma, ya yi sanadin mutuwar mutane 26.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanda aka kashe sun haɗa da dakarun rundunar ƴan sa-kai, ƴan sanda huɗu, da mutane 20.

Kankara: Gwamna Radda ya yi ta'aziyya

A wata sanarwa da gwamnatin Katsina ta fitar a shafin X, Malam Raɗɗa ya miƙa sakon ta'aziyya da alhini ga dangi da abokan arzikin waɗanda suka rasa rayukansu sakamakom harin.

Ya kuma bi sahun daukacin mazauna jihar wajen yin addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma ba iyalansu haƙuri da juriya.

Gwamnan ya kuma yabawa jami'an tsaro bisa koƙarin da suke ci gaba da yi wajen tunƙarar miyagun ƴan bindiga da suka zama barazana ga zaman lafiya a jihar.

Gwamnatin Radda za ta tunkari lamarin tsaro

Kara karanta wannan

"Za a iya ƙarar da ƴan bindiga a mako 2," Gwamna ya tona halayen ƴan sanda da sojoji

Dikko Raɗɗa ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kawar da ayyukan ƴan bindiga da duk wasu nau'ikan miyagun laifuka a sassan jihar Katsina.

A sanarwar mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran gwamna, Ibrahim Kaula, ya ce harin da ƴan bindiga suka kai Kanƙara koma baya ne a yaƙi da matsalar tsaro.

Kaula ya ce:

"Gwamna Raɗɗa ya roki duk wanda ke da bayanai kan waɗanda suka kai wannan hari ya zo ga hukuma, ya jaddada cewa zai yi duk mai yiwuwa don hukunta maharan."

A ƙarshe, Malam Dikko ya buƙaci Katsinawa su kwantar da hankalinsu kuma su ci gaba da baiwa jami'an tsaro haɗin kai domin kawo ƙarshen waɗannan ƴan ta'adda.

Gwamna Lawal ya koka da halin sojoji

A wani rahoton kuma Gwamnan Zamfara ya nuna damuwa kan yadda sojoji da ƴan sanda suka sa wasa a lamarin yaƙi da ƴan bindiga a Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Gwamnan Plateau ya cire dokar hana fita da ya sanya, ya fadi dalili

Dauda Lawal ya ce halayyar jami'an tsaron waɗanda ke karkashin gwamnatin tarayya ne ya sa shi kafa rundunar asakarawan Zamfara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel