"An Maida Rai ba Komai ba," Atiku Ya Riga Shugaban Kasa Ta'aziyyar Kisan Katsina

"An Maida Rai ba Komai ba," Atiku Ya Riga Shugaban Kasa Ta'aziyyar Kisan Katsina

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana takaicin yadda gwamnati ta gaza magance matsalar tsaro duk da makudan kudin da ake fitarwa bangaren
  • Atiku Abubakar, wanda tsohon dan takarar shugaban kasa ne a jam'iyyar PDP na wannan batu ne biyo bayan kisan wasu mutane 20 da'yan bindiga su ka yi a Katsina
  • Wasu 'yan ta'adda ne su ka kai hari garin Yargoje a jihar Katsina tare da kashe mutane da dama ciki har da mata da yara, yayin da su ka farmaki motar jami'an tsaro

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Tsohon dan takarar shugaban kasar nan, Atiku Abubakar ya bayyana takaicin yadda aka mayar da ran ‘yan kasar nan ba a bakin komai ba.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya faɗi hanya 1 da za a ceto Najeriya daga halin da ta shiga

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Yargoje da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina da ya kashe mutane 20.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya caccaki yadda gwamnati ke tunkarar tsaro a Najeriya Hoto: AbdulRasheeth Shehu
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar wanda tsohon mataimakin shugaban kasar nan ne ya yi Allah wadai da yadda ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Gwamnati ta kasa maganin rashin tsaro,’ Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce alamu na nuna gwamnatin tarayya ta gaza magance matsalar tsaro.

Tsohon dan takarar shugaba kasar nan na ganin duk da makudan kudin da gwamnati ke cewa tana fitarwa saboda tsaro, har yanzu bata sauya zani ba.

Vanguard News ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya ce harin ya munana, kuma ya jefa shi cikin alhinin kashe bayin Allah ciki har da yara kanana.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da babban malamin addini a Kaduna, rundunar 'yan sanda ta magantu

Atiku na ganin daga cikin abubuwan takaicin shi ne yadda har ‘yan binigar su ka kai hari kan motocin jami’an tsaro tare da kashe wasu a cikinsu.

Atiku ya magantu kan manufofin Tinubu

A baya mun kawo muku labarin cewa dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya bayyana cewa manufofin shugaban kasa Bola Tinubu sun gaza kai Najeriya ga ci.

Atiku Abubakar ya ce tsare-tsaren da Tinubu ya bijiro da su sun kara jefa Najeriya cikin talauci, saboda haka ne ya shawarce shi kan dawo da martabar kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel