An Samu Raguwar Kudin FAAC da Gwamnatocin Kasar nan Suka Raba a Watan Mayu
- Asusun kasafin kudin Najeriya (FAAC) ya bayyana cewa ya raba wa gwamnatocin kasar nan a matakai uku N1.14trn a watan Mayu, 2024 domin gudanar da ayyuka
- An samu kudin ne daga harajin da gwamnati ta tara na EMTL, VAT da sauransu, amma an samu raguwar kudin da aka raba idan aka hada da na watan Afrilu
- A sakon da FAAC ta fitar bayan taronta na wannan Yuni wanda ministan harkokin tattalin arziki Wale Edun ya jagoranta, an samu raguwar kudin da N60bn
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Asusun kasafin kudin Najeriya ya raba N1.14trn tsakanin gwamnatocin tarayya da jihohi da kananan hukumomi a watan Mayu, 2024.
Kudin da aka raba ya ragu da N60bn idan aka kwatanta da wanda gwamnatin ta raba tsakanin rassanta a wayan Afrilu.
The Cable ta wallafa cewa asusun kasafin kudin (FAAC) ne ya bayyana haka a sakon daya fitar na watan Yuni bayan taron da ministan harkokin tattalin arziki, Wale Edun ya jagoranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
FAAC ta bayyana yadda aka samu kudin
Sanarwar bayan taron ta bayyana cewa an samu kudin shiga na N1.143trn, inda aka samo N157.183bn daga kudin doka, sai N463.425bndaga aka samu na harajin VAT.
Sanarwar ta kara da cewa an samu kudin shiga nan N15.146bn daga harajin kudin sakon aika kudi ta wayar hannu (EMTL) da N507.456bn na harajin da aka samu daga musayar kudin kasashen waje.
Asusun FAAC ya tabbatar da samun kudin shiga da ya kai N2.32trn a watan Mayu kamar yadda Vanguard News ta wallafa.
Kudin da aka raba daga harajin
An raba harajin tsakanin gwamnatocin kasar nan a mataki guda uku da ya hada da gwamnatin tarayya da ta samu N60bn.
Gwamnatocin jihohin kasar nan sun samu N30.9bn yayin da kananan hukumomi su ka samu N23.8bn.
FAAC ta raba 1.1trn a watan Janairu
A baya kun samu labarin yadda asusun kasafin kudin kasar nan (FAAC) ya bayyana cewa ya raba N1.1trn ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da kananan hukumomi.
A taron da ministan harkokin tattalin arziki ya jagoranta, an bayyana cewa an samu kudaden da aka raba daga harajin VAT, EMTL da sauransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng