Niger: An Shiga Dimuwa Bayan ’Yan Bindiga Sun Shammaci Sojoji, Sun Raunata Jami'ai

Niger: An Shiga Dimuwa Bayan ’Yan Bindiga Sun Shammaci Sojoji, Sun Raunata Jami'ai

  • Dakarun sojoji sun sake gamuwa da matsala bayan harin 'yan bindiga a karamar hukumar Rafi da ke jihar Niger
  • Lamarin ya faru ne a jiya Litinin 10 ga watan Yuni inda maharan suka shammaci sojojin a sansaninsu
  • Shugaban karamar hukumar, Ayuba Usman Katako ya tabbatar da hakan inda ya ce sojoji biyu sun samu raunuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - Akalla sojoji biyu ne suka samu munanan raunuka bayan 'yan bindiga sun farmaki dakarun a jihar Niger.

Maharan sun shammaci sojojin ne a sansaninsu a karamar hukumar Rafi da ke jihar a jiya Litinin 10 ga watan Yuni.

'Yan bindiga sun kuma kai farmaki kan dakarun sojoji a Niger
'Yan sun raunata sojoji 2 yayin wani hari a Niger.
Asali: Original

Niger: 'Yan bindiga sun farmaki dakarun sojoji

Kara karanta wannan

Duk da dokar hana masu ciki aikin Hajji, Hajiyar Najeriya ta haifi jaririn farko a Makkah

Daily Trust ta tattaro cewa maharan suna kokarin wucewa karamar hukumar Wushishi ne zuwa Mashegu lokacin da suka kai harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar da cewa daya daga cikin maharan ya rasa ransa yayin artabu da jami'an tsaro a yankin, cewar Punch.

Watanni biyu da suka gabata, 'yan bindiga sun hallaka sojoji biyu a wani kwanton bauna da suka yi kan sojoji a karamar hukumar Shiroro.

Hukumomi sun tabbatar da faruwar harin Niger

Shugaban karamar hukumar Rafi, Alhaji Ayuba Usman Katako ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya nuna damuwa sosai.

Katako ya ce sojojin suna ci gaba da karbar kulawa kuma suna samun sauki a asibitin kwararru na IBB da ke birnin Minna.

Ya bukaci addu'o'i da kuma goyon baya daga jama'a domin ba jami'an tsaro damar dakile matsalar hare-haren 'yan bindiga a fadin jihar baki daya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ɓarna, sun tafi da matafiya da yawa a hanyar zuwa Abuja

'Yan bindiga sun hallaka mutane a Niger

A wani labarin, kun ji cewa aƙalla mutum bakwai ne ƴan bindiga suka kashe a wani sabon harin ta'addanci da suka kai a jihar Neja.

Miyagun ƴan bindigan sun kai harin ne a wasu ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar inda suka kona gidaje da dabbobi.

Maharan da ake zargin ƴan ta’adda ne sun fille kawunan biyu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, Kabiru Salihu da Abubakar Karaga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel