Kungiyoyin Kwadago Za Su Koma Yajin Aiki a Ranar Talata? An Bayyana Gaskiya

Kungiyoyin Kwadago Za Su Koma Yajin Aiki a Ranar Talata? An Bayyana Gaskiya

  • Ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta musanta cewa za ta ci gaba da yajin aikin da ta tsagaita wanda take yi kan sabon mafi ƙarancin albashi a ranar Talata, 11 ga watan Yuni
  • Chris Onyeka, mataimakin babban sakataren NLC na ƙasa, ya ce bayanin da ya yi a hirar da aka yi da shi, ba a fahimce shi da kyau ba
  • Kwamred Onyeka ya bayyana cewa abin da kawai ya ce shi ne ƙungiyar za ta yi taro biyo bayan kammala tattaunawar da kwamitin mafi ƙarancin albashin ya yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta musanta cewa za ta koms yajin aikin da take yi kan mafi ƙarancin albashi a ranar Talata, 11 ga watan Yunin 2024.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya samo mafita ga gwamnati kan mafi karancin albashi

Ƙungiyar ta ce rahotannin da ake yaɗawa kan batun komawa yajin aikin babu ƙamshin gaskiya a cikinsu.

'Yan kwadago sun musanta batun komawa yajin aiki
NLC ta musanta batun komawa yajin aiki a ranar Talata Hoto: @NLCHeadquarters, @officialABAT
Asali: Twitter

A cewar ƙungiyar, an sauya ma'anar abin da mataimakin babban sakataren ƙungiyar NLC na ƙasa, Chris Onyeka, ya faɗi a hirar da aka yi da shi a ranar Litinin, 10 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene gaskiya kan batun komawa yajin aiki?

A wata hira ta wayar tarho da jaridar Tribune, Chris Onyeka, ya bayyana cewa ba a fahimci kalamansa da kyau ba.

"Bidiyon tattaunawar da na yi da masu gabatarwa a shirin tashar Channels tv yana nan domin tabbatar da cewa ɓan taɓa cewa ƴan ƙwadago na iya komawa yajin aiki a ranar Talata ba."
"Sun tambaye ni ko ƴan ƙwadago za su koma yajin aikin gama gari da suka tsagaita."
"Na gaya musu cewa tun da gwamnati da ƴan ƙwadago sun amince su kammala tattaunawa cikin mako ɗaya, kuma wannan mako ɗayan zai ƙare a ranar Talata, ƙungiyoyin ƙwadagon za su yi zama kan tattaunawar domin samar da matsayarsu."

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Kungiyoyin kwadago sun caccaki gwamnonin Najeriya

"Wannan ita ce amsar da na ba su, na yi mamaki yadda labarai ke yawo cewa na ce za a koma yajin aiki a ranar Talata."

- Chris Onyeka

Ƴan ƙwadago da gwamnati sun kasa cimma matsaya

Har yanzu kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya ba su cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata ba.

Yayin da gwamnatin tarayya ta yi tayin za ta biya N62,000, ƴan ƙwadagon sun dage a kan sai an biya N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Matsayar ƴan ƙwadago kan albashi N62,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta bayyana cewa ba za ta ƙarbi tayin N62,000 ko N100,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi na ma’aikatan Najeriya ba.

Ƙungiyar ta haƙiƙance kan cewa sai dai gwamnati ta biya N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel