Zargin Rashawa: Kotu Ta Ba EFCC Sabon Umarni Kan Yunƙurin Kama Rabiu Kwankwaso

Zargin Rashawa: Kotu Ta Ba EFCC Sabon Umarni Kan Yunƙurin Kama Rabiu Kwankwaso

  • Jam'iyyar NNPP, da jagoranta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wasu mutane shida sun shigar da hukumar EFCC kara a gaban kotu
  • Bangarensu Sanata Kwankwaso sun nemi kotun ta dakatar ta da EFCC daga kamawa, tsarewa, gayyata ko hantarar su
  • A zaman kotun na yau Litinin, Mai shari'a YU Muhammad ya amsa wannan rokon, inda ya hana EFCC ta kama Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Wata babbar kotu a jihar Kano mai zamanta a cikin sakatariyar Audu Bako ta dakatar da hukumar EFCC daga gayyata, tuhuma, tsarewa ko hantarar Rabiu Musa Kwankwaso.

Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso
Kotu ta hana EFCC ta kama Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Facebook

Jam'iyyar NNPP, Dr. Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Chif Clement Anele, Lady Folshade Aliu, Injiniya Buba Galadima da Sanata Rabiu Kwankwaso ne suka shigar da karar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta ɗauki zafi, an dakatar da wasu manyan jiga jigan jam'iyya

EFCC: Kotu ta amsa bukatar su Kwankwaso

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa babbar kotun ta hana EFCC ta dauki wani mataki kan jagoran jam'iyyar NNPP da wasu mutane bakwai kan zargin da take yi masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar da ke yaki da masu yiwa dukiyar al'umma zagon kasa (EFCC) kadai ake kara a shari'ar, kuma ita kadai aka hana ta tuhumi Kwankwaso a yanzu.

Mai shari'a Yusuf Ubale Muhammad ne ya ba da wannan umarnin na wucin gadi bayan da ya karanta bukatar da masu shigar da karar suka gabatar a ranar 5 ga watan Yunin 2024.

Kotu ta hana EFCC ta kama Kwankwaso

Mai shari'a Yusuf ya ce:

"Kotu ta ba da wannan umarnin ga wanda ake ƙara. Kotu ta haramta wa wanda ake kara, ko jami'anta, ko wakilanta daga kama wadanda suka shigar da karar.

Kara karanta wannan

Kano: Kwankwaso ya fadi abin da ya dauke hankalin Abba a shekara 1 na mulki

"Kotun ta ba da umarnin ka da a kama, ko a tsare, ko a gayyaci wadanda ake kara ko a hantare su ko a muzguna masu, har sai an kammala wannan shari'ar."

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Yunin 2024.

Jirgin shugaban kasar Malawi ya bace

A wani labarin, mun ruwaito cewa jirgin sama dauke da mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Klaus Chilima ya bace.

Wata sanarwa da ofishin shugaban kasa da ministocin Malawi ya fitar ta ce duk wani kokari na tuntubar jirgin ya ci tura amma ana kan nema.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel