'Yan Majalisa Na Neman Mayar da Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya Ya Zama 2

'Yan Majalisa Na Neman Mayar da Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya Ya Zama 2

  • Kudurin neman a sauya wa'adin shugaban kasa da gwamnoni zuwa zango daya mai shekaru shida ya tsallake karatu na farko
  • Majalisar wakila na neman a samar da ofishin mataimakan shugaban kasa guda biyu daga sassan Kudu da Arewacin Najeriya
  • Majalisar ta ce za ta yi amfani da ikon da ke kanta wajen yin dokokin da za su bunkasa Najeriya da saita tsarin siyasar kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta gabatar da shawarar samar da ofishin mataimakan shugaban kasa guda biyu daga sassan Kudu da Arewacin Najeriya.

Har ila yau, Majalisar wakilai ta gabatar da shawarar yin wa'adin mulki daya tal na shekaru shida ga shugabannin kasa da gwamnoni.

Kara karanta wannan

Bayan canja taken ƙasa, Tinubu zai karɓi ƙudurin sauya tsarin mulkin Najeriya

Wakilan tarayyar Najeriya.
Yan majalisa na neman a mayar da ofishin mataimakin shugaban kasa ya zama biyu. Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa 'yan majalisa 35 ne suka gabatar da kudurorin doka guda shida da suka tsallake karatu na farko a zauren majalisar kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufar takaita wa'adin shugaban kasa

Mai magana da yawun 'yan majalisu 35 masu ra'ayi ɗaya, Ikenga Imo Ugochinyere (Ideato ta Arewa/Kudu) ya bayyana fa'idojin kudurorin idan har suka zama doka.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, Hon. Ugochinyere ya ce kudurorin za su rage yawan kudin tafiyar da gwamnati, inganta tsarin mulki da kuma samar da daidaito a ƙasa.

Ya ce 'yan majalisar za su yi amfani da ikon da ke kansu wajen yin dokokin da za su bunkasa Najeriya da kuma saita tsarin siyasar kasar, inji rahoton The Guardian.

Samar da ofishin mataimakan shugaba kasa

A cewar Hon. Ugochinyere, akwai bukatar samar da ofishin mataimakan shugaba kasa biyu wadanda za su fito daga shiyyar Kudu da Arewa.

Kara karanta wannan

Kudurin ƙirƙirar sabuwar jiha a Kudu maso Gabas ya wuce karatun na 1 a majalisar wakilai

"Ya zama cewa shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa na 1 su fito daga shiyya daya, mataimaki na 2 ya fito daga ɗayar shiyyar.
"Haka zalika, mataimakin shugaban kasa na 1 zai zama shugaban ƙasa idan shugaban kasar da ke kai ba zai iya ci gaba da jan ragamar kasar ba. Amma duka mataimakan za su zama ministoci ne."

- 'Dan majalisar wakilan.

Gwamnonin Arewa maso Yamma sun gana

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun saka labule a Gidan Legas da ke Ikeja, bayan samun tarba daga Gwamna Babajide Sanwo-Olu.

Ana sa ran taron na kungiyar gwamnonin Kudu maso Yamma zai tattauna batutuwan da suka shafi shiyyar da ma Najeriya baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel