Jerin Gwamnonin da Suka Biya Ma'aikata Albashi Saboda Zuwan Babbar Sallah

Jerin Gwamnonin da Suka Biya Ma'aikata Albashi Saboda Zuwan Babbar Sallah

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

A ranar Lahadi mai zuwa 16 ga watan Yuni, 2024 al'ummar Musulmi za su yi Babbar Sallah (Eid-el-Kabir) kamar yadda fadar sarkin Musulmi ta sanar.

Ana kuma kiran wannan idi da Sallar Layya saboda ibadar yankan dabba don Allah da musulmi ke yi a wannan lokaci.

Gwamna Radda da Ahmed Aliyu.
Gwamnoni sun fara rabawa ma'aikata goron Sallah Hoto: @Dikko_Radda, @Ahmedaliyu
Asali: Twitter

Sai dai a bana sallar ta zo a tsakiyar wata wanda hakan ya sa wasu gwamnoni musamman a Arewa suka fara ƙoƙarin taimakawa ma'aikata domin su yi shagali cikin wadata.

Legit Hausa ta tattaro maku jerin jihohin da suka yiwa ma'aikatan su wani tanadi/biyan albashi domin su yi shagalin sallah cikin wadata da farin ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana ranakun hutun Babbar Sallah a Najeriya

Jihar Katsina

A wani mataki na inganta walwalar ma'aikata, Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bayar da umarnin biyan ma'aikata N45,000 a matsayin rance/goron sallah.

Gwamnan, wanda ya tabbatar da haka a shafinsa na X, ya ce kuɗin sun kunshi rancen N30,000 da za a cire a albashin ma'aikata cikin wata uku da N15,000 goron Sallah.

"A lokacin da shagulgulan babbar Sallah ke ƙara matsowa na ɗauki matakan inganta walwalar ma'aikata, na umarci a biya kowane ma'aikaci N45,000 a matsayin rance/goron Sallah."
"Za mu cire N30,000 a albashin ma'aikata a watannin Yuli, Agusta da Satumba, watau N10,000 kenan kowane wata yayin da N15,000 kuma goron Sallah ne."

- Malam Dikko Raɗɗa.

Jihar Sokoto

A maƙwambciyar Katsina, Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya amince da biyan albashin watan Yuni ga ma’aikata a jihar daga ranar Litinin.

Gwamna Aliyu ya ɗauki wannan matakin ne domin ba su damar tunkarar babbar Sallah cikin farin ciki da walwala.

Kara karanta wannan

Gwamna ya waiwayi ma'aikata, ya bayar da umarnin a tura masu kuɗi kafin Babbar Sallah

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Abubakar Bawa, ya fitar kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Bawa ya bayyana cewa matakin zai haɗa da ma'aikatan ƙananan hukumomi da na jiha da ƴan fansho.

Sanarwar ta ƙara da cewa Gwamna Aliyu na taya ɗaukacin al'ummar Musulmi murna da fatan alheri yayin da suke shirye-shiryen shagalin Babbar Sallah.

Jihar Yobe

Gwamna Mai Mala Buni ya bayar da umarnin biyan ma'aikata albashin watan Yuni domin su shirya zuwan bikin Babbar Sallah.

Babban sakataren ofishin shugaban ma'aikatan jihar, Alhaji Bukar Ƙilo ne ya bayyana haƙa a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu.

Ya ce Mai Girma Buni ya umurci ma'aikatar kuɗi da kananan hukumomi su tura wa ma'aikata haƙƙinsu na watan Yuni kafin ranar Sallah.

A cewarsa, wannan na ɗaya daga cikin gatan da gwamna ke nunawa ma'aikata domin inganta walwala da jin daɗinsu.

Kara karanta wannan

Ana shirin bikin sallah, tsofaffin ma'aikatan KEDCO sun rufe kamfanin a Kano

Jihar Nasarawa

Gabanin babban Sallah da za a yi ranar 16 ga watan Yuni, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ba da umarnin biyan ma'aikatan jihar albashin watan Yuni.

Gwamna Sule ya bayar da wannan umarni ne yayin da yake jawabi a wurin taron raba tallafi da gwamnatinsa ta shirya ranar Talata, Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan ya umarci shugabannin kananan hukumomin jihar 13 da su yi amfani da kudaden da suka tara wajen biyan albashin ma’aikata kafin ranar Sallah.

Falalar kwanakin watan Dhul Hijjah

A wani rahoton kuma babban malamin addinin Islama, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ja hankalin musulmin duniya kan yawaita ayyukan alheri a cikin wannan wata na Zul-Hijja.

A cikin wani bidiyo da ya watsa a shafinsa na Facebook, wanda Legit.ng Hausa ta samu, malamin ya bayyana falalar dake tattare da watan Zul-Hijja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel