Dakarun Sojoji Sun Gwabza Fada da 'Yan Bindiga a Kaduna, an Hallaka Miyagu

Dakarun Sojoji Sun Gwabza Fada da 'Yan Bindiga a Kaduna, an Hallaka Miyagu

  • Dakarun sojojin Najeriya na Operation Whirl Punch sun gagarumar nasara kan ƴan bindiga masu tada ƙayar baya a jihar
  • Sojojin sun hallaka ƴan bindigan ne a yankin Dantarau da ke ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar a yayin wani aikin sintiri
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakarun sojoji na Operation Whirl Punch sun kashe ƴan bindiga biyar a yankin Dantarau na ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Dakarun sojojin sun je wani aikin sintiri ne a yankin Kachia-Kajuru a lokacin da suka ci karo da ƴan bindigan.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga a Katsina, sun ceto mutanen da aka sace

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Kaduna
Sojoji sun hallaka 'yan bindiga biyar a Kaduna Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka hallaka ƴan bindiga

Ya kuma ce ƴan bindigan da suka yi artabu da dakarun sojojin sun samu munanan raunuka, yayin da ya gargaɗi mutane da kada su ba da magani ga mutanen da su yarda da su ba, ba tare da sanar da jami'an tsaro ba.

Ya bayyana cewa dakarun sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, bindiga ƙirar gida guda ɗaya, jigidar AK-47 guda tara, harsasai masu kaurin 7.62mm guda 250, babura guda biyu da rediyo guda biyu, cewar rahoton Punch.

Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa dakarun sojojin sama na Operation Whirl Punch sun kai hare-hare a sansanonin ƴan bindiga a Sabon Birnin Daji a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani hatsabibin ɗan bindiga a Zariya, ya fara tona asirin wasu

"Dakarun sojojin sun fara aikin sintiri domin share yankin Maro-Enugu wanda ya fara daga ƙananan hukumomin Kachia zuwa Kajuru."
"A ƙauyen Dantarau, sojojin sun ci karo da ƴan bindiga, bayan an yi musayar wuta, an hallaka ƴan bindiga mutum biyar."

- Samuel Aruwan

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) da ke aiki a 'Operation Lake Sanity 2' ta ce ta kashe ƴan ta’adda 140.

Rundunar ta kuma bayyana cewa sojoji shida sun rasa rayukansu yayin faɗa da ƴan ta'addan a yankin tafkin Chadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel