Kungiyoyin Kwadago Sun Ba Gwamnoni Shawara Kan Mafi Karancin Albashi

Kungiyoyin Kwadago Sun Ba Gwamnoni Shawara Kan Mafi Karancin Albashi

  • Ƙungiyoyin ƙwadago sun nuna ɓacin ransu kan kalaman gwamnonin Najeriya na cewa ba za su iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba
  • Ƙungiyoyin ƙwadagon sun buƙaci duk gwamnan da ya san ba zai iya biyan mafi ƙarancin albashi ba ya yi murabus daga muƙaminsa
  • Hakan na zuwa ne dai yayin da ake ci gaba da tattauna da ƴan ƙwadago da wakilan gwamnati kan sabon mafi ƙarancin albashin da za a riƙa biyan ma'aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun yi martani kan gwamnonin Najeriya bayan sun nuna ba za su iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba.

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun bayyana cewa kalaman na gwamnonin ba su dace ba yayin da ake tsaka da tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin da gwamnati za ta riƙa biyan ma'aikata.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Kungiyoyin kwadago sun caccaki gwamnonin Najeriya

NLC, TUC sun caccaki gwamnonin Najeriya
Kungiyoyin kwadago sun bukaci gwamnoni su yi murabus kan mafi karancin albashi Hoto: @NGFSecretariat
Asali: Twitter

Gwamnonin a ƙarƙashin ƙungiyar gwamnonin Najeriya sun ƙi amincewa da shirin biyan mafi ƙarancin albashi na N60,000 ga ma’aikatan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani NLC, TUC ta yi wa gwamnoni?

Sai dai, ƙungiyoyin ƙwadagon sun caccaki matsayar ta gwamnonin inda suka buƙaci duk gwamnan da ba zai iya biyan mafi ƙarancin albashin ba ya yi murabus daga muƙaminsa.

Da yake magana da jaridar The Punch a ranar Lahadi, mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, Tommy Etim, ya bayyana cewa:

"Babu mafi ƙarancin albashi. Ya kamata a aiwatar da kowane ɓangare na yarjejeniyar."
"Ga gwamnoni, mun faɗi hakan a fili cewa idan ba za ku iya biyan mafi ƙarancin albashi ba, ku yi murabus saboda an zaɓe ku domin gudanar da mulki ba domin samar da ababen more rayuwa kawai ba."
"Idan aka samar da ababen more rayuwa sannan ba mutanen da za su yi amfani da su, wanene zai yi amfani da su? Lokacin da suke yaƙin neman zaɓe sun gaya mana hakan? Ba su gaya mana hakan ba."

Kara karanta wannan

"Kuɗin sun yi yawa" Gwamnoni sun mayar da martani kan sabon mafi ƙarancin albashi

"Sun yi amfani da talakawa wajen samun mulki amma da zarar sun cimma burinsu sai su fara wasu tunane-tunane marasa kan gado."

Mafi ƙarancin albashin da gwamnati za ta biya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa kan mafi ƙarancin albashi da za ta iya biya ga ma'aikatan Najeriya.

Bayan doguwar ganawa da aka yi, a ƙarshe Shugaba Bola Tinubu ya bayyana N62,000 a matsayin mafi karancin albashi da gwamnatin za ta biya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel