Sanusi II Ya Ragargaji Gwamnatin Tarayya Bayan Dawowa Mulki? an Gano Gaskiya
- An yi bincike kan gaskiyar wani faifan bidiyo da ake yadawa cewa Sanusi II ya soki gwamnati bayan dawowa kujerar sarautar Kano
- A faifan bidiyon an gano Sanusi II yana caccakar Gwamnatin Tarayya tare da cewa babu mai yi musu bazara komai girmansa a kasar
- Sai dai binciken kwa-kwaf ya tabbatar da cewa bidiyon ya kwana biyu domin an nade shi ne tun a shekarar 2022 a Lagos
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - An yi ta yaɗa wani faifan bidiyo inda aka gano Muhammadu Sanusi II na sukar Gwamnatin Tarayya.
A cikin maganganunsa, Sanusi II ya ja hankalin gwamnatin da ta yi kokarin kawo sauyi a Najeriya.
Bidiyon Sanusi II da ake yaɗawa
Wani mai amfani da kafar X, @Row_Haastrup shi ya wallafa bidiyon inda ya ce Sanusi II ya yi wannan jawabi ne bayan dawowa kujerar sarautar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kalamai masu tsauri da ratsa zuciya daga Sanusi Lamido Sanusi bayan dawowa kujerar sarautar Kano."
- Cewar mawallafin
Binciken kwa-kwaf kan bidiyon Sanusi II
Sai dai an yi bincike ta amfani da 'Google reverse image' wanda ya tabbatar da cewa bidiyon ya dade tun shekarar 202 aka nade shi..
An gano cewa Sanusi II ya yi wannan jawabi ne tun a watan Agustan shekarar 2022 a Lagos yayin wani babban taro.
Yayin taron a Lagos, Sanusi II ya ce babu wani mai yi musu barazana ko da kuwa gwamna ne ko shugaban kasa.
"Babu wanda zai yi mana barazana ko gwamna ko shugaban kasa da ba za mu fada maka cewa ya yi kuskure ba."
"Mun kama wani layi ne daban, amma da siyasa muka shiga da watakila zan iya zama gwamna ko shugaban kasa."
- Muhammadu Sanusi II
Dubban Kanawa sun tarbi Aminu Ado
Kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya sake gudanar da sallar Juma’a a ranar 7 ga watan Yuni a jihar.
Dubban jama’a ne suka tarbi sarkin yayin da ya ke dawowa daga masallacin Juma’a duk da shari’ar da ake yi.
Asali: Legit.ng