Ana Tsaka da Aikin Hajji, Musulmai Sun Bukaci Tinubu Ya Kori Jami'ar NAHCON

Ana Tsaka da Aikin Hajji, Musulmai Sun Bukaci Tinubu Ya Kori Jami'ar NAHCON

  • Kungiyar Concerned South-South Muslims ta nemi taimakon Bola Tinubu kan sauya sunan wata wakiliyar hukumar NAHCON a yankin
  • Kungiyar ta bukaci Tinubu da ya janye sunan Zainab Musa a yankin ganin rashin alakarta da Kudu maso Kudancin Najeriya
  • An nada Zainab ne domin wakiltar hukumar NAHCON a yankin Kudu maso Kudu inda kungiyar ta ce matar ta fito daga yankin Arewa maso Gabas ne

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

JIhar Cross River – Kungiyar Musulmai a yankin Kudu maso Kudancin Najeriya ta tura bukata ga Bola Tinubu kan hukumar alhazai.

Kungiyar ta bukaci Tinubu ya sauya sunan Zainab Musa da ke wakiltar NAHCON a yankin tun da ba daga can ta fito ba.

Kara karanta wannan

"Abin da ya sa Bola Tinubu ya fi Atiku da Obi cancantar zama shugaban ƙasa a 2023"

Musulmai sun roki Tinubu ya sallami wakiliyar NAHCON
Kungiyar Musulmai sun roki Tinubu ya kori wakiliyar NAHCON, Zainab Musa daga Kudu maso Kudu. Hoto: @DOlusegun.
Asali: Twitter

Musulmai sun tura bukata ga Tinubu

Wannan na kunshe ne a cikin watan sanarwa da wakilin kungiyar, Abdullahi Abdulhaleem ya sanyawa hannu da Legit ta leko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi ya bukaci daukar matakin cire sunanta ganin cewa ta fito daga jihar Gombe a yankin Arewa maso Gabas.

Ya ce ba ta da alaka da Kudu maso Kudancin kasar ta bangaren haihuwa ko aure da kuma ‘yan uwa a can.

Kungiyar Musulmai sun yi barazana kan lamarin

Har ila yau, kungiyar ta yi bazazanar daukar mataki idan har ba a janye sunan Zainab ba daga mukamin.

Ta kuma bukaci shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya shiga lamarin tare da janye mukamin da aka ba ta.

Kungiyar ta ce nadin Zainab a matsayin wakiliyar NAHCON a yankin ya saba ka’ida musamman ganin rashin alakarta da Kudu maso Kudu.

Kara karanta wannan

Kasar Saudiyya ta kama masu damfarar mutane domin sama musu izinin aikin hajji

Wannan na zuwa ne yayin da mahajjata ke kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajji.

Hajiya daga Niger ta rasu a Saudiyya

A wani labarin, kun ji cewa wata Hajiya daga jihar Neja mai suna Ramatu Abubakar ta riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki.

Hajiyar mai shekara 45 a duniya ta rasu ne a birnin Madinah na ƙasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin bana.

Wannan mutuwa ba ita ce ta farko ba, akalla an sanar da rasuwar mutane 'yar Najeriya hudu a kasar Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.