Mafi Karancin Albashi: Kungiyoyin Kwadago Sun Caccaki Gwamnonin Najeriya

Mafi Karancin Albashi: Kungiyoyin Kwadago Sun Caccaki Gwamnonin Najeriya

  • Ƙungiyoyin kwadago sun yi Allah wsdai da kalaman gwamnonin Najeriya na cewa ba za su iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba
  • Ƙungiyoyin na NLC da TUC sun bayyana kalaman a matsayin zallar mugunta inda suka buƙace su da su sake tunani
  • Sun yi nuni da cewa gwamnonin sun manta da cewa rayuwa ta yi tsada a ƙasar nan sakamakon tsige tallafin man fetur

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun caccaki gwamnonin Najeriya 36 kan cewa ba za su iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba.

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun bayyana kalaman na gwamnonin kan ma'aikata a matsayin mugunta yayin da suka buƙace su da su sake tunani.

Kara karanta wannan

'Yan ƙwadago na shirin ɗaukar mataki bayan Gwamnatin Tinubu ta miƙa tayin N62,000

NLC ta caccaki gwamnoni
NLC ta caccaki gwamnoni kan mafi karancin albashi Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Facebook

A ranar Juma'a ne dai ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta hannun daraktan yaɗa labaranta, Hajiya Halimah Salihu Ahmed ta ce ba za su iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani NLC ta yiwa gwamnoni?

Da yake martani kan kalaman gwamnonin, daraktan yaɗa labarai na NLC, Benson Upah, ya ce gwamnonin sun manta da yadda rayuwa ta yi tsada a ƙasar nan, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Ya yi nuna da cewa gwamnonin sun manta da yadda farashin man fetur, Dala da sauran abubuwa suka yi tashin gwauron zabi.

"Mun damu matuƙa kan kalaman da suka fito daga ƙungiyar gwamnoni cewa gwamnonin jihohi ba za su iya biyan N60,000 a matsayin mafi karanci albashi ba saboda wasu jihohin za su riƙa ciyo bashi domin biyan albashi a kowane wata."

Kara karanta wannan

"Kuɗin sun yi yawa" Gwamnoni sun mayar da martani kan sabon mafi ƙarancin albashi

"Mun yi amanna cewa abin da gwamnonin suka yi bai dace ba. Bai kamata waɗannan kalaman su fito ba yayin da ake tsakiyar tattaunawa. Sam hakan bai dace ba."

- Benson Upah

"Gwamnoni sun samu ƙarin kuɗaɗe", NLC

Ƴan ƙwadagon sun bayyana cewa kuɗaɗen da ake ba gwamnonin daga asusun gwamnatin tarayya sun ƙaru daga N700bn zuwa N1.2trn wanda hakan ya sanya lalitarsu ta cika yayin da talakawa ke shan wuya.

A cewarsu abin da gwamnonin ya kamata su yi domin su iya biyan mafi ƙarancin albashi (ba N60,000 ba) shi ne su rage kashe kuɗaɗe a gwamnati, rage cin hanci tare da ɗaukar walwalar ma'aikata da muhimmanci.

Batun mafi ƙarancin albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Doyin Okupe, ya caccaki dokar mafi karancin albashi ta ƙasa.

Okupe ya soki dokar bisa wajabtawa gwamnonin jihohin Najeriya 36 su riƙa biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi a jihohinsu daidai da na gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng