Ana Rigimar Mafi Karancin Albashi, Naira Ta Fado a Kasuwa Bayan Dala Ta Sake Ƴunkurawa
- Darajar Naira ta fadi a kasuwannin Najeriya bayan samun habaka na wasu kwanaki yayin da dala ta tashi
- A jiya Juma'a 7 ga watan Yuni an siyar da dala kan N1,483 sabanin N1,481 a ranar Alhamis 6 ga watan Yuni a kasuwanni
- Rahoton FMDQ ya tabbatar da cewa hakan ya nuna darajar Naira ta fadi da 0.16% kenan wato N2.50 a jiya Juma'a 7 ga watan Yuni
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Yayin da ake ci gaba da hada-hadar ƴan canji a Najeriya, Naira ta yi ƙasa a kasuwa.
Darajar dala ta tashi a kasuwa bayan siyar da ita kan N1,483 a jiya Juma'a 7 ga watan Yuni.
Naira: Dala ta sake yunkurawa a kasuwa
Raho ton FMDQ ya tabbatar da cewa darajar Naira ta fadi da N2.50 idan aka kwatanta da ranar Alhamis 6 ga watan Yuni, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan faduwa na darajar Naira ya nuna ta samu nakasu da 0.16% idan aka kwatanta da ranar Alhamis din makon da ya wuce.
Dala: Yadda Naira ta zube a kasuwa
A ranar Alhamis 6 ga watan Yuni an siyar da dala kan N1,481.49 sabanin jiya Juma'a da kasa siyar kan N1,483.99.
Har ila yau, yawan daloli da ke kasuwa ya karu daga $213.31m a ranar Lahadi zuwa $269.27m a jiya Juma'a 7 ga watan Yuni.
Hakan na zuwa ne bayan galaba da Naira ta samu kan dala tsawon kwanaki a kasuwannin 'yan canji.
Naira tayi kasa bayan dala ta tashi
A wani labarin, kun ji cewa darajar kudin Najeriya wanda muka fi sani da Naira ta ragu a kasuwar hada-hadar kuɗi ta gwamnati ranar Talata 4 ga watan Yuni.
Dalar Amurka ta ƙara tsada, inda ta koma N1,476.95 kan kowace Dala guda a kasuwar gwamnati jiya.
Bayanai daga shafin kula da hada-hadar musayar kuɗin waje FMDQ na ranar Talata ya nuna cewa ƙimar Naira ta ragu da Kobo 83.
Asali: Legit.ng