Katsina: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari, Sun Kashe Gomman Mutane a Garuruwa 13

Katsina: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari, Sun Kashe Gomman Mutane a Garuruwa 13

  • Miyagun ƴan bindiga sun kai kazaman hare-hare kan bayin Allah a ƙananan hukumomin Safana da Dutsinma a jihar Katsina
  • Ganau sun bayyana cewa ana fargabar maharan sun kashe akalla mutane 30 yayin da wasu da dama suka tsere suka bar gidajensu
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq ya tabbatar da an kai hare-hare a garin Dutsinma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Ana fargabar aƙalla mutane 30 ne suka mutu sakamakon wasu hare-hare da ƴan bindiga suka kai kauyuka a kananan hukumomin Dutsinma da Safana a Katsina.

Ƙananan hukumomin Dutsinma da Safana na cikin yankuna da ke sahun gaba waɗanda ƴan bindiga suka matsa da kai hare-hare duk da kokarin jami'an tsaro da gwamnatin Katsina.

Kara karanta wannan

Ministoci 3 da manyan jiga-jigai sun shiga taron kwamitin mafi ƙarancin albashi a Abuja

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
Yan bindiga sun aikata mummunar ta'asa a kauyuka 13 a jihar Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

'Yan bindiga sun shiga kauyukan Katsina

Ganau da abin ya faru a kan idonsu sun shaidawa Channels tv ta wayar tarho cewa maharan sun kai farmaki aƙalla kauyuka 13 a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun jero sunayen ƙauyukan da suka hada da Dogon Ruwa, Sabon Gari Unguwar Banza, Tashar Kawai Mai Zurfi, Sanawar Kurecen Dutsi, da Unguwar Bera.

Sauran su ne Kurecin Kulawa, Larabar Tashar Mangoro, Sabaru, Ashata, Unguwar Ido, Kanbiri, Kunamawar Mai Awaki da Kunamawar ‘Yargandu.

A cewarsu, ƴan bindiga sun shiga waɗannan kauyuka sun aikata ta'asa a ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024, Daily Trust ta ruwaito.

Katsina: Ƴan bindiga sun tarwatsa jama'a

Ganau sun ƙara da cewa munanan hare-haren sun firgita al'ummar da ke rayuwa a waɗannan kaiyukan, waɗanda galibi sun koma ƴan gudun hijira a Dutsinma.

Wani mutumi da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a Arewa, sun kashe yan sanda da mutane da asuba

"Ko a yanzu da nake magana da ku, mun samu labarin ƴan bindiga sun sake kai farmaki ƙauyukan Lezumawa, ‘Yar Kuka, Rimi da Dogon Ruwa."

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, ya tabbatar da kai sababbin hare-haren a karamar hukumar Dutsinma.

"Eh gaskiya ne, amma ba ni da cikakken bayani kan kai hari a karamar hukumar Safana, zan dawo gare ku nan ba da jimawa ba," in ji shi.

Ƴan bindiga sun kashe kansila

Kuna da labarin wasu miyagun ƴan bindiga sun kashe kansila da shugaban matasa a kauyen Isu da ke ƙaramar hukumar Onicha a jihar Ebonyi.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun tare mutanen biyu, suka bude masu wuta sai da suka tabbatar sun mutu, sannan suka gudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel