Kotu Ta Hukunta DSTV da GOtv, Ta Umarci a Haskawa Ƴan Najeriya Tashoshin Kallo Kyauta

Kotu Ta Hukunta DSTV da GOtv, Ta Umarci a Haskawa Ƴan Najeriya Tashoshin Kallo Kyauta

  • Wata kotu da ke zamanta a Abuja ta dauki mataki kan kamfanin Multichoice na DSTV da GOtv bayan kara kudi ga abokan huld
  • Kotu ta ci tarar kamfanin N150m tare da umartarsa da ya ba ƴan Najeriya damar kallo ba tare da biya ba har tsawon wata daya
  • Wannan na zuwa ne bayan kamfanin ya kara kuɗin da ake biya kafin kallon tashoshinsa wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Mayu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun sauraron kararraki da koken abokan hulda, ta ci tarar kamfanin Multichoice da ke da DSTV da GOtv N150m.

Kotun ta kuma umarci kamfanon ya ba ƴan Najeriya damar kallon tashoshinsa kyauta na tsawon wata daya.

Kara karanta wannan

Mutane 8 sun mutu yayin da aka yi asarar dukiyar da ta kai N31.6m a jihar Kano

Kotu ta ci tarar DSTV da GOtv N150m kan kara kudin tashoshi
Kotu ta ci tarar DSTV da GOtv N150m bayan kara kudin tashoshi ba bisa ka'ida ba. Hoto: Pius Utomi Ukpei.
Asali: Getty Images

Karin kudi: Hukuncin kotu kan DSTV, GOtv

Mai shari'a, Thomas Okosu wanda ya jagoranci alkalai uku shi ya yanke wannan hukuncin bayan wani lauya ya maka kamfanin a kotu, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan mai suna Festus Onifade shi ya maka kamfanin a kotu bayan kara kudin da suka yi wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Mayu.

Har ila yau, kotun ya dakatar da Multichoice daga karin kudin ga kwastomominsa inda ta ce hakan saba doka ne, The Nation ta tattaro.

Hukumar FCCPC ta zargi kamfanin da kara kudin ba tare da ankarar da abokan hulda wata daya kafin sanarwar ba.

Martanin DSTV da GOtv kan shari'ar

Sai dai Multichoice ya kalubalanci hukumar FCCPC inda ya ce ikon kayyade farashi ya rataya ne kan shugaban kasar Najeriya.

Har ila yau, alkalin kotu ya ce a sashe na 39(2) na dokar FCCPC kotun tana da damar shiga duka lamari kan sha'anin kasuwanci.

Kara karanta wannan

TCN ya kammala gyaran wuta a Arewa maso gabas bayan kwanaki babu lantarki

"Wannan kotu tana da damar kutsawa cikin duka harkokin kasuwanci da ke gudana a Najeriya."

- Thomas Okosu

Kotun ta kuma yi Allah wadai da karin kudi da Multichoice ya yi yayin da ta zargi kamfanin da saba dokar kotun.

Kotu ta hana karin kudin DSTV, GOtv

Kun ji cewa kotu ta haramtawa Kamfanin Multichoice Nigeria Limited kara farashin kayayyakinsa da ya kudurta daga ranar 1 ga Afrilu.

Kotun mai mambobi uku a karkashin jagorancin Thomas Okosun, ta bayar da wannan umarni ne biyo bayan wata karar da lauya Festus Onifade ya gabatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.