Kudurin Ƙirƙirar Sabuwar Jiha a Kudu Maso Gabas Ya Wuce Karatun Na 1 a Majalisar Wakilai

Kudurin Ƙirƙirar Sabuwar Jiha a Kudu Maso Gabas Ya Wuce Karatun Na 1 a Majalisar Wakilai

  • Kudirin neman kirkirar sabuwar jiha a yankin Kudu maso Gabas ya tsallake karatu na farko a zauren majalisar wakilai
  • Jihar idan aka kirkire ta, za a sanya mata suna 'Jihar Orlu', mai babban birninta a Orlu, kamar yadda rahotanni suka bayyana
  • Dan majalisar Ideato ta Arewa da ta Kudu, Hon. Ikenga Ikeagwuonu Ugochinyere, da wasu 'yan majalisu 15 ne suka gabatar da kudirin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta dauki mataki na samar da sabuwar jiha a shiyyar siyasar yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

A zaman majalisar na ranar Alhamis, ‘yan majalisar sun amince da kudirin dokar kafa jihar Orlu, wanda ya tsallake karatu na farko, da jiran karatu na biyu.

Kara karanta wannan

'Dan majalisar wakilai da ya kai wa gwamnan PDP ziyara ya shiga matsala, ana tuhumarsa

Majalisar wakilan Najeriya kan kirkirar sabuwar jiha
Majalisar wakilai ta gabatar da kudurin kirkirar sabuwar jihar Najeriya. Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Kirkirar jiha zai sauya kundin mulki

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, dan majalisa mai wakiltar mazabar Ideato ta Arewa/Ideato ta Kudu a jihar Imo, Ikenga Ugochinyere da wasu 'yan majalisa 15 ne suka gabatar da kudurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar daftarin kudirin, samar da jihar Orlu zai sauya kundin tsarin mulkin kasar na 1999 (da aka sabunta), wanda zai kara yawan jihohin tarayya daga 36 zuwa 37, in ji jaridar Guardian.

Daga ina za a kirkiro sabuwar jihar?

Kudirin yana neman shigar da sabon sakin layi a kasan sunan jihar Ondo, gabanin sakin layin jihar Osun, inda zai zama kamar haka: Jiha – Orlu, babban birnin – Orlu, in ji The Punch.

Za a samar da sabuwar jihar ne daga jihohin Imo, Abia, da Anambra, inda Orlu zai zama babban birninta.

Kara karanta wannan

Basaraken Arewa ya sha da ƙyar a hannun 'yan bindiga, 'yan sanda sun kai masa ɗauki

Kananan hukumomi a karkashin jihar Orlu

A cewar kudurin dokar da aka gabatar, kananan hukumomin da za su zama a karkashin jihar da ake son a kirkira sun hada da:

Orlu, Orsu, Oru ta Yamma, Oru ta Gabas, Ideato ta Arewa, Ideato Kudu, Njaba, Nkwerre,Nwangele, Isu, Oguta, Ohaji, Egbema, Onuimo, Ihiala, Uga da Ihiala.

Sauran sun hada da: Uli, Ozubulu, Akokwa, Arondizuogu, Umuchu, Umunze, Umuaku, Sabuwar Ideoto ta Arewa, Nwabosi ta Yamma, Nwabosi ta Gabas, Owerre Nkworji, Alaoma, Amaifeke, da kuma Owerrebiri Umuowa.

Majalisar wakilai za ta tuhumi mambanta

A wani labarin mun ruwaito cewa majalisar wakilai za ta binciki Hon. Ikenga Ugochinyere (PDP, Imo) bayan ya kai wa gwamnan Rivers ziyarar ban girma.

Hon. Yusuf Adamu Gagdi (APC, Plateau) ne ya nemi majalisar da ta tuhumi Hon. Ikenga kan abin da ya kira 'keta alfarma' saboda ya nuna cewa ziyarar ta 'majalisar ce gaba daya."

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel