Yadda abin yake: Majalisar Dattawa ta yi karin haske a kan batun kirkiro sababbin Jihohi 20

Yadda abin yake: Majalisar Dattawa ta yi karin haske a kan batun kirkiro sababbin Jihohi 20

  • ‘Yan Majalisa sun musanya rade-radin da ke yawo a kan kirkirar sababbin Jihohi
  • Kakakin Majalisar Dattawa, Ajibola Basiru, yace ba su amince a karo jihohi 20 ba
  • Sanata Ajibola Basiru yake cewa doka ta tanadi yadda ake kirkirar jiha a Najeriya

Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta yi maza ta yi magana game da rade-radin da ake yi a kan kudirin kirkiro wasu sababbin jihohi a kasar nan.

Sanatocin sun bada shawara a karo wasu jihohi 20?

Majalisar dattawan ta ce ta samu takardun roko daga al’umma, suna neman a kirkiro karin jihohi, amma ta ce ita ba ta bada shawarar ayi hakan ba.

The Cable ta ce mai magana da yawun Sanatocin Najeriya, Ajibola Basiru, ya fitar da jawabi a kan wannan a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, 2021.

Kamar yadda jaridar ta bayyana, Sanatocin sun ce ba su da hurumin da za su bada wannan shawarar ba tare da an bi jerin wasu matakai ba tukun.

Kara karanta wannan

2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari

“Abin bai kai ga bada shawarar a kirkiro wata jiha ba, kwamitin majalisa ya karbi kudiri da-dama da ke neman a kawo wasu jihohi, ya zartar da cewa ba zai bada shawara a kirkiri wata jiha ba har sai an bi sashe na 8 na kundin tsarin mulkin Najeriya."

Kakakin Majalisar Dattawa
Sanata Ajibola Basiru Hoto: www.arise.tv
Asali: UGC

Wani tanadi dokar kasa ta yi kan kirkirar jiha?

Abin da sashe na takwas na kundin tsarin mulkin kasar ya ce shi ne; Za a kirkiri sabuwar jiha ne idan

a. Akalla kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar da ke wakiltar yankin da ke da wannan bukata sun yarda da hakan -

i. Majalisar dattawa da na wakilan tarayya da

ii. Majalisar dokokin jihar da ke wannan roko, da

iii. Kananan hukumomin wannan yanki sun je gaban majalisa

b. Neman kirkirar sababbin jihohi ya samu karbuwa ta hanyar kuri’ar da kashi biyu cikin uku na wannan yanki su ka kada domin ayi hakan.

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

c. Sai mafi yawan ‘yan majalisun dokoki da na tarayya su amince da wannan kuri’a da aka yi.

d. Daga nan sai a amince da kudirin bayan an samu kashi biyu cikin uku na kowace majalisa sun yarda.

Sanata Ajibola Basiru yake cewa abin da su ka yi shi ne kai maganar gaban hukumar zabe na INEC, domin ta tabbatar an bi jerin wadannan dokokin kasa.

Jihohin da ake nema a kirkiro sun hada da; ITAI, Katagum, Okura, Adada, Gurara, Ijebu, Tiga, Amana, Gongola, Mambila, Savannah, Okun, da irinsu Orashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng