Ina aka kwana kan batun kirkirar jihohi?

Ina aka kwana kan batun kirkirar jihohi?

- Najeriya kasa ce mai ban sha'awa kunshe da yarika daban daban

- Akwai kusan yarika 371 a Najeriya

- Jihohi 36 ne amma ba lokaci daya aka kirkire su ba

Ina aka kwana kan batun kirkirar jihohi?
Ina aka kwana kan batun kirkirar jihohi?
Asali: UGC

Najeriya kasa ce mai ban sha'awa kunshe da yarika daban daban. Daga arewa zuwa yamma akwai al'adu daban daban wadanda ke bayyana kansu cike da ban sha'awa. Haka ma daga gabas zuwa yamma.

Akwai kusan yarika 371 a kasar, sannan da jihohi 36. Ba'a kirkiri jihohin a lokaci daya ba, sai dai anyi su ne daya bayan daya.

A baya, gwamnatin Goodluck Jonathan, taso ta qara jihohi ta hannun majalisun Tarayya da jihohi, sai dai ba kamar soja ba, lamarin ya sami sarkakiya, inda har aka kusa shiga zabe a 2014, lamarin bai kammalu ba.

Sanata David Mark, shugaban Majalisa na wancan karon, yasha alwashin sake dawo da batun muddin jama'a suka zabe su suka zarce a 2015, lamari da bai yiyu ba, kuma har yanzu batun ya mutu.

DUBA WANNAN: Hakkin yara: Ina gwamnatoci ne, da har yanzu limamai ke sanya wa yara laqanin maita?

Ina aka kwana kan batun kirkirar jihohi?
Ina aka kwana kan batun kirkirar jihohi?
Asali: UGC

A takaice a 1960 zuwa 1966 babu wata jiha. Akwai yankunan arewa, yamma, gabas da yamma ta tsakiya.

Kirkirar jihohi an fara ne a 1967 da Janar Yakubu Gowon ya hau mulkin kasar. Ya kashe yankunan tare da kirkiro jihohi 12.

Bayan kusan shekaru 10 sai Janar Murtala Ramat Mohammed ya kara jihohi 7 akan 12.

Shekaru 11 bayan nan, karkashin mulkin Janar Ibrahim Badamosi Babangida, aka kara jihohi biyu.

A shekarar 1987 bayan kirkiro jihohin, Najeriya ta samu jihohi 21.

A 1991 ne Janar Babangida ya kara jihohin zuwa 31. Janar din a 1996 ya maida jihohin zuwa 36.

Ko yaya batun zai farfado? Sai masu neman neman jihohin suma sun farfado da batun ga shuwagabanninsu.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng