'Dan Majalisar Wakilai da Ya Kai Wa Gwamnan PDP Ziyara Ya Shiga Matsala, Ana Tuhumarsa

'Dan Majalisar Wakilai da Ya Kai Wa Gwamnan PDP Ziyara Ya Shiga Matsala, Ana Tuhumarsa

  • Majalisar wakilai ta umarci kwamitinta mai kula da da’a da gata da ya binciki wani mamba mai suna Ikenga Ugochinyere (PDP, Imo)
  • Kwamitin zai binciki Hon Ugochinyere kan zargin keta alfarmar majalisa da ya yi a lokacin wata ziyara da ya kai wa Siminalayi Fubara
  • Hakan ya biyo bayan wani korafin keta alfarma da dan majalisar wakilai, Hon. Yusuf Adamu Gagdi (APC, Plateau) ya gabatar a zaure

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta shirya tuhumar wani dan majalisa, Hon. Ikenga Ugochinyere, mamba mai wakiltar mazabar Ideato na jihar Imo.

A zamanta na ranar Alhamis, majalisar ta mika Hon. Ikenga Ugochinyere ga kwamitin da'a da gata domin tuhumarsa kan ziyarar da ya kai wa gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan

"Yadda 'yan bindiga suka yi ta'adi a jeji, haka El-Rufai yayi a ofis a Kaduna" - Sanata

Majalisar wakilai ta yi zama ranar Alhamis a Abuja
Majalisar wakilai za ta tuhumi manmbanta kan kai wa Fubara ziyara. Hoto: @IkengaImo
Asali: Twitter

'Dan majalisa daga jihar Filato, Hon. Yusuf Gagdi ne ya gabatar da bukatar inda ya zargi Hon. Ugochinyere da 'bata suna majalisar', in ji rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meya faru ake tuhumar dan majalisar?

A watan da ya gabata, Hon. Ugochinyere ya jagoranci 'yan majalisar wakilai sama da 50 zuwa bikin cika shekara daya na gwamnatin Fubara a Port Harcourt a babban birnin Rivers.

Hon. Ugochinyere, dan jam’iyyar PDP ne mai goyon bayan Fubara kuma ya bayyana kansa a matsayin mai magana da yawun ‘yan majalisar adawa 60.

A ranar 4 ga watan Yuni, Hon. Ugochinyere ya wallafa bidiyon ziyarar da suka kai a shafinsa na X.Hon

Yayin da yake gabatar da bukatar, Gagdi ya ce an keta alfarmarsa a matsayinsa na dan majalisar dokoki saboda Ugochinyere ya ce ‘yan majalisar sun kai ziyarar a madadin majalisar.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta yiwa Tinubu gata, ta amince ya naɗa shugaban hukumar SEC

Majalisar wakilai za ta binciki Ugochinyere

Hon. Gagdi ya ce bayan ziyarar da ya kai wa Fubara, Hon. Ugochinyere ya fitar da wata sanarwa da ta nuna cewa tawagar ta wakilci majalisar wakilai a ziyarar.

“Ba laifi ba ne a kai ziyarar nuna goyon baya, amma ba daidai ba ne a nuna cewa tawagar na wakiltar kafatin majalisar. Ina fatan majalisar za ta duba wannan lamari."

- Hon. Yusuf Gagdi.

Mataimakin kakakin majalisar, Ben Kalu wanda ya jagoranci zaman ya mika batun ga kwamitin da'a da kuma gata.

NNPP ta dakatar da dan takarar gwamna

A wani labarin, mun ruwaito cewa NNPP a Edo ta dakatar da ɗan takarar ta na gwamnan jihar, Azemhe Ezena kan zargin kin biyayya ga jam'iyyar.

Wannan dakatarwar da Azemhe Ezena ya yi watsi da ita na zuwa ne ana saura watanni uku a yi zaben gwamnan jihar Edo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.