Atiku Abubakar ya Bankado 'Dalilin' Ɓoye Ɓoyen Gwamanti kan Tallafin Fetur

Atiku Abubakar ya Bankado 'Dalilin' Ɓoye Ɓoyen Gwamanti kan Tallafin Fetur

  • Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kokarin ɓoye gaskiya shi ya sa ta ƙi fitowa ta yi bayani kan tallafin fetur
  • Atiku Abubakar wanda ya yi zawarcin kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP ya ce akwai alamun gwamnati na karkatar da kudin 'yan Najeriya
  • Ya yi zargin cewa rahotanni sun ce har yanzu ana biyan tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana soke shi ranar da ya sha rantsuwar aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Tinubu ta ƙi bayyana kuɗin da aka kashe a kan tallafin man fetur saboda wasu dalilai. Ɗan takarar shugaban kasar nan karkashin jam'iyyar PDP a kakar zaɓen da ya gabata ya ce gwamnati na karkatar da kudin al'umma zuwa aljihun ɗaiɗaikun su.

Kara karanta wannan

"Karya ne," Gwamnati ta yi magana kan amincewa da biyan albashin akalla N105, 000

Atiku Abubakar
Tallafin fetur: Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Tinubu da karkatar da kudin 'yan Najeriya Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Atiku Abubakar ya sake tabo Bola Tinubu

Daily Trust ta tattaro cewa zargin na ƙunshe cikin sanarwar da hadimin Atiku Abubakar, Paul Ibe ya fitar a makon nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya ce babbar alamar da ke tabbatar da zargin karkatar da kuɗin al'umma shi ne yadda gwamnatin ta ƙi fitar da bayanai kan batun.

Atiku: "Kuɗin tallafin fetur ya ƙaru"

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana kaɗuwa kan samun labarin har yanzu gwamnati na biyan tallafin man fetur duk da shugaba Bola Tinubu ya soke shi a ranar 29 Mayu, 2023.

Ya ce an gano cewa a 2024, kudin tallafin fetur da aka ware ya kai ₦5.4trn maimakon ₦3.6trn da aka biya a 2023, kamar yadda The Cable ta wallafa.

Tuni hadimin shugaban kasa Bayo Onanuga ya ce babu batun tallafin man fetur a kasar nan.

Kara karanta wannan

NLC na neman ƙarin albashi, Tinubu ya bayyana wani muhimmin aiki da zai yi zuwa 2030

"Tinubu ya gaza," Atiku Abubakar

A wani labarin kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta gaza kawo wani ci gaba a kasar nan.

Atiku Abubakar na wannan bayani ne yayin da Bola Ahmed Tinubu ya shekara guda cir yana mulkin Najeriya bayan nasara a zaben 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.