Basaraken Arewa Ya Sha da Ƙyar a Hannun ’Yan Bindiga, ’Yan Sanda Sun Kai Masa Ɗauki

Basaraken Arewa Ya Sha da Ƙyar a Hannun ’Yan Bindiga, ’Yan Sanda Sun Kai Masa Ɗauki

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta yi nasarar dakile wani hari na yin garkuwa da Sarkin Ninzo, Alhaji Umar Musawa
  • A ranar Laraba ne wasu 'yan bindiga suka kai wa basaraken farmaki da nufin sace shi, amma Allah ya sa ya tsallake rijiya da baya
  • An ruwaito cewa an nemi uwar gidan basaraken an rasa bayan wannan farmaki amma 'yan sanda sun baza jami'ai domin nemo ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - Wani basaraken Arewacin Najeriya ya sha da ƙyar a lokacin da wasu gungun 'yan bindiga suka kai masa farmaki da nufin sace shi.

'Yan bindiga sun kai wa basarake hari a Kaduna
'Yan sanda sun dakile harin da 'yan bindiga suka kai wa basake a Kaduna. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da cewa ta daƙile harin da 'yan bindigar suka kai wa Sarkin Ninzo, Alhaji Umar Musa.

Kara karanta wannan

Masarautun Kano: Kotu ta dauki mataki kan shari'ar da ake yi bayan zamanta a yau

Matar basarake ta ɓata bayan harin

Masarautar Ninzo na a karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna, kuma an kai harin ne a ranar Laraba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa har yanzu ba a san inda mai ɗakin basaraken take ba.

Mansir ya ce tuni aka tura jami'an tsaro zuwa dazuzzukan da ke yankin Sanga domin nemo uwar gidan basaraken.

Garkuwa da basarake: Kungiya ta yi Allah wadai

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kungiyar raya yankin Ninzo ta yi Allah wadai da wannan hari da 'yan bindigar suka kai na yin garkuwa da Alhaji Umar Musa.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Farfesa Moses Audi da sakataren kungiyar, Silas Anche suka fitar, sun roki jami'an tsaro su ceto mai dakin basaraken.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ƴan bindiga sun kutsa fadar sarki inda suka yi awon gaba da matarsa

Kungiyar ta kuma roki al'ummar masarautar Ninzo da su kwantar da hankula tare da ba jami'an tsaro hadin kai yayin gudanar da binciken su.

"A bar El-Rufai ya kare kansa" - Lauya

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani lauya mai kare hakkin dan Adam, Mike Ozekhome ya yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta ba Nasiru El-Rufai damar kare kansa.

Majalisar jihar Kaduna ta zargi tsohon gwamnan da karkatar da N423bn da cin zarafin ofis, inda ta nemi a tuhumi shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel