'Yan Kwadago Na Jiran Tsammani, An Mikawa Tinubu Sabon Tsarin Albashi

'Yan Kwadago Na Jiran Tsammani, An Mikawa Tinubu Sabon Tsarin Albashi

  • A yau Alhamis, 6 ga watan Yuni wa'adin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba ministan kudi kan karin albashi ya cika
  • Kungiyoyin kwadago sun zuba ido su ga me zai bayyana daga fadar shugaban kasa domin daukar mataki kan tattaunawar da suka fara
  • A jiya Laraba kungiyar kwadago ta sanar da cewa ba za ta karbi kari kadan da ba zai biyawa ma'aikata bukatun yau da kullum ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigerian - A yau Alhamis wa'adin da shugaban kasa Bola Tinubu ya ba ministan kudi, Wale Edun na kawo jadawalin karin albashi ya cika.

Kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun dakatar da tattaunawa da gwamnatin tarayya kan karin albashi zuwa cikar wa'adin.

Kara karanta wannan

Gwamnati na shirin janye harajin shigo da kaya, ana sa ran saukar farashin abinci

Yajin aikin kwadago
Ministan kudi zai mika tsarin karin albashi ga shugaba Tinubu. Hoto: NLC Nigeria|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kungiyar kwadago ta ce samun sakamakon da ministan kudi zai fitar yana da muhimmanci dangane da tattaunawar da ake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsammanin 'yan kwadago a kan karin albashi

Wani dan kungiyar kwadago da ke cikin kwamitin tattaunawa ya bayyana cewa suna tsammanin sakamako mai kyau daga bayanan da ministan zai fitar a yau.

'Dan kwadagon da ya nemi a boye sunan shi ya kuma kara da cewa bayanan da ministan zai fitar za su taimaka sosai wajen cigaba da tattaunawa da suke da gwamnati.

Tinubu ya ba minista sa'o'i 48

Kamar yadda Legit ta ruwaito, shugaban kasa Bola Tinubu ya ba ministan kudi sa'o'i 48 domin fitar da yadda karin albashin zai kasance.

Shugaban kasar ya ba ministan wa'adin ne bayan kungiyar kwadago ta janye yajin aikin mako daya domin cigaba da tattaunawa da gwamnati.

Kara karanta wannan

Jonathan ya bayyana abu 1 da zai hana 'yan siyasa zuwa kotu idan sun fadi zabe

Ministan yada labarai da wayar da kan al'umma, Idris Muhammad ya ce za su cigaba da hada kai da kungiyar kwadago wajen samar da ƙarin albashi cikin mako daya.

Ministan ya kuma tabbatar wa yan kwadago cewa lallai da su da gwamnati duk abu daya ne, ba wai abokan gaba ba ne.

Daga baya aka samu labari cewa rahoton tsarin albashin ya shiga fadar shugaban kasa.

Yajin aiki: Mawaki ya yi asara sosai

A wani rahoton, kun ji cewa yajin aikin kasa da awanni 48 da 'yan kwadago suka yi a Najeriya ya shafi fitaccen mawakin nan, Folarin Falana wanda aka fi sani da Falz Falz.

Rahotanni sun nuna cewa Falz Falz ya ce ya yi asarar dukkanin kudin da ya kashe wajen shirya daukar wani bidiyo saboda ya gaza komawa Legas daga Uyo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng