Aikin Hajjin 2024: NDLEA Ta Kama Alhazan Najeriya Dauke da Hodar Iblis a Legas

Aikin Hajjin 2024: NDLEA Ta Kama Alhazan Najeriya Dauke da Hodar Iblis a Legas

  • Hukumar yaƙi da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta samu nasarar kama maniyyata aikin Hajjin bana dauke da hodar Iblis
  • Jami'an hukumar sun kai samame otel din da alhazan hudu suke zaune inda aka kama su suna shirin haɗiye ledoji 200 na hodar
  • NDLEA ta ce za ta tsaurara bincike kan alhazan Najeriya da ke fakewa da zuwa aikin Hajji domin safarar ƙwayoyi zuwa Saudiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Legas - Jami'an hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLE) sun kama maniyyata aikin Hajjin 2024 dauke da hodar Iblis a jihar Legas.

An ce jami'an sun kai samame otel din Emerald da ke Ladipo, a karamar hukumar Oshodi a jihar inda su ke zama kafin jirgin su ya tashi zuwa Saudiya a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

NLC na neman ƙarin albashi, Tinubu ya bayyana wani muhimmin aiki da zai yi zuwa 2030

NDLEA ta kama maniyyata a Legas
NDLEA ta kama alhazan Najeriya dauke da hodar Iblis a Legas. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

Kamar yadda hukumar ta wallafa hotuna da bidiyon maniyyatan a shafinta na X, ta ce za ta ci gaba da kama masu fakewa da zuwa aikin Hajji domin yin safarar miyagun ƙwayoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama maniyyata 4 da hodar Iblis

Maniyyatan da aka kama su ne: Usman Kamorudeen, Olasunkanmi Owolabi, Fatai Yekini, da wata mata, Ayinla Kemi.

An ce masu laifin sun kama dakuna biyu a cikin otel din inda suka shirya ledoji 200 na hodar Iblis, kowacce leda na da nauyin kilo 2.20 domin ba su damar haɗiye wa.

Jami'an NDLEA da suka kai samame dakunan biyu, sun kama ledoji 100 a kowanne daƙi, kuma ana zaton maniyyata biyu ne za su haɗiye ledojin 200.

NDLEA za ta tsaurara binciken maniyyata

Shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) ya jinjinawa jami'an hukumar na Legas.

Kara karanta wannan

PDP ta watsawa Atiku ƙasa a ido kan hadaka da Kwankwaso, Obi, ta yi alfahari

Buba Marwa ya ce hukumar za ta ci gaba da tsaurara bincike kan maniyyatan da za su je aikin Hajjin bana domin kama wadanda ke safarar miyagun ƙwayoyi.

Shugaban hukumar na NDLE ya ce Najeriya na aiki da Saudiya domin tabbatar da cewa wadanda aka shirya za su karbi kwayoyin a can ƙasar su ma an kama su.

Kalli bidiyon maniyyatan a nan kasa:

Hajj: Alhazai miliyan 1 sun isa Saudiya

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumomi a Saudiya sun ce zuwa ranar Lahadin da ta gabata, alhazai miliyan daya ne suka shiga ƙasar domin gudanar da aikin Hajjin 2024.

Haka zalika hukumomin ƙasar sun ce sun ƙirƙiri wani kwagirin kuɗi na zamani wanda alhazai za su rika amfani da shi a yayin gudanar da aikin Hajjin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.