Sanusi II vs Aminu Ado: Halin da Ake Ciki a Kano Yayin da Kotu Ta Fara Zaman Shari'a a Kano

Sanusi II vs Aminu Ado: Halin da Ake Ciki a Kano Yayin da Kotu Ta Fara Zaman Shari'a a Kano

  • An jibge jami'an tsaro a harabar babbar kotun tarayya da ke Kano yayin da aka fara sauraron ƙarar rushe sababbin masarautun Kano
  • Jami'an tsaro na ƴan sanda da na DSS sun hana ababen hawa wucewa ta kan hanyar titin da ke zuwa kotun bayan sun jibge motocinsu a kusa da kotun
  • Kotun za ta saurari ƙarar da aka shigar ne dai wacce ta ƙalubalanci dokar rushe sababbin masarautun Kano da majalisar dokokin jihar ta amince da ita

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - An tsaurara matakan tsaro a harabar babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano yayin da aka fara sauraren ƙarar rikicin masarautar Kano.

An jibge jami'an tsaro na ƴan sanda da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a kusa da kotun.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Aminu: NLC ta kawo babban cikas a a kotu kan rigimar sarautar Kano

An tsaurara matakan tsaro a Kano
An jibge jami'an tsaro a kotu yayin fara zaman karar masarautar Kano Hoto: Aminu Ado Bayero, Sanusi Lamido Sanusi
Asali: Facebook

An tsaurara tsaro a Kano saboda shari'a

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan sanda da jami'an DSS sun ajiye motocinsu a wurare masu muhimmanci a kusa da kotun, inda suka hana yin zirga-zirga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin yanzu, an sauya hanyar da ababen hawa ke bi ta kan titin 'Court Road' zuwa 'Zoo Road' a unguwar Gyadi-Gyadi.

Yajin aikin da aka fara a faɗin ƙasar nan kan mafi ƙarancin albashi ya shafi zaman babbar kotun tarayya da ke Kano kan umarnin da ta ba da na hana naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Kotu ta umarci hana rushe masarautun Kano

Babbar kotun tarayyar da ke Kano ta bayar da umarnin dakatar da gwamnatin jihar Kano daga aiwatar da dokar da ta rushe sababbin masarautun Kano.

Mai shari’a Mohammed Liman ya bayar da umarnin a ƙarar da Sarkin Dawaki Babba na masarautar Kano, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwan da suka faru a majalisar dattawa a makon da ya gabata

An shirya fara gudanar da zaman sauraron ƙarar a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni da misalin ƙarfe 10 na safe, amma an ɗaga lokacin.

Sarkin Kano, Sanusi II ya ba da shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa babu kasar da za ta ci gaba matuƙar ana take gaskiya da adalci a shari'a.

Basaraken da aka mayar kan sarauta kwanan nan ya faɗi haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin buɗe taron kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA).

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel