Gwamnan Kano, Abba Ya Taimaki Talakawa Sama da 460 Masu Talla a Titi

Gwamnan Kano, Abba Ya Taimaki Talakawa Sama da 460 Masu Talla a Titi

  • Gwamnatin jihar Kano a karkashin Abba Kabir Yusuf ta ware makudan kudi domin tallafawa masu karamin karfi su kara jari
  • Mai magana da yawun gwamnatin jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da haka yayin taron kaddamar da tallafin
  • An ware masu sana'o'i daban-daban domin ba ba su tallafin saboda bunkasa tattalin arzikin su da kawo cigaba a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta dauki damarar tallafawa masu ƙananan sana'o'i domin haɓaka tattalin arziki.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba ya raba tallafi ga masu sana'a. Hoto: Sanusi Batue Dawakin Tofa
Asali: Facebook

Jaridar the Guardian ta ruwaito cewa an ware masu ƙananan sana'o'i da suke ƙoƙarin neman na kan su ne domin a tallafa musu.

Kara karanta wannan

Mutane 8 sun mutu yayin da aka yi asarar dukiyar da ta kai N31.6m a jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda za su mori tallafin

Rahotanni sun nuna cewa yawanci wadanda aka ware domin moran tallafin masu sayar da kayan adon mota ne da kayan madafi.

Kuma an zabe su saboda yadda suke hada-hada tsakanin 'yan daba a kan titunan jihar amma duk da haka ba su gajiya ba.

Meyasa gwamnatin Kano ta kawo tallafin?

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa dama yana daga cikin manyan manufofin ta tallafawa masu kananan sana'o'i a Kano.

Dawakin Tofa ya ce burin Gwamna Abba ne tallafawa mata da matasa domin ganin sun samu abin dogaro da kai, kuma saboda haka ne ya kirkiro tallafin.

Wane tallafi aka ba masu sana'o'in?

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa an ba kowane daga cikin masu kananan sana'o'in su 465 tallafin kudi N50,000.

Gwamnatin ta kashe kudi sama da Naira miliyan 23 domin tallafawa mutanen da suka fito daga yankuna daban-daban a cikin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ma'aikatan gwamnati a jihar Kano sun bi umarnin kungiyoyin NLC da TUC

An biya 'yan fansho a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya cika alkawarin da ya dauka na ci gaba da biyan ‘yan fansho bashin da suke bin gwamnati.

Rahotanni sun nuna cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da ba da umarnin kaddamar da biyan Naira biliyan 5 ga 'yan fansho a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel